Kishi ya tashi ana tsakiyar biki yayin da wani Banufe ya auri ‘Yan Matansa 2 a lokaci 1
- Ana ta labarin Mohammed Alfa Mohammed a kafafen sada zumunta a dalilin auren da ya yi da mata biyu
- Alhaji Mohammed Alfa ya angwance da matansa - Adama Ahmad Mohammed da Aisha Ismail Mohammed
- An ga kishin daya daga cikin amaren wannan Bawan Allah yayin da ake rawa a wajen bikin da aka yi a Bida
Niger - Wani Mohammed Alfa ya angwance da matansa biyu a lokaci guda Malama Adama Ahmad Mohammed da Malama Aisha Ismail Mohammed.
Legit.ng Hausa ta samu labari cewa ana yin wannan gagarumin aure ne a garin Bida, jihar Neja.
Abin da ya sa ake labarin wannan aure shi ne angon zai auri mata biyu a lokaci guda. A addinin musulunci babu laifi namiji ya tara mata har hudu a aure daya.

Kara karanta wannan
Dakarun Soji Sun Damke ‘Yan Ta’adda 79, Masu Taimaka Musu da ‘Yan Matan Chibok 2, DHQ
An fara biki tun ranar Laraba, 22 ga watan Disamba, 2021, inda aka yi taron mata a gidan daya daga cikin amaren a unguwar Low Cost a garin Bida, jihar Neja.
A kowane taro an yi ta cashewa da wakokin Nufawa.

Source: UGC
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kamar yadda katin bikin ya nuna an fara aurawa Mohammed Mohammed Alfa sahibarsa Adama Ahmad Mohammed ne a yau Juma’a da safe a gidan iyayenta.
An shafa fatiha a ranar Juma'a
Bayan sallar Juma’a sai aka sake daurawa wannan Ango aure da dayar sahibar ta sa, Aisha Ismail Mohammed. Hakan ya sa ya tabbata a matsayin mai mata biyu.
A ranar Asabar aka shirya liyafa ta musamman tare da bikin nuna al’adun gargajiya. An kira manyan mawaka da ake ji da su a kasar Nufawa domin su yi wasa.
A wani bidiyo da yake yawo a Twitter da Instagram, an ga kishin amaren ya fara tashi yayin da Alhaji Mohammed Alfa ya rike su domin su yi rawa a wajen biki.
Asali: Legit.ng