Jami’an tsaro sun tsinci gawan ‘Dan Sarki da wata mata tsirara haihuwar-uwarsu a mota
- Dakarun So-Safe Corpes sun ci karo da gawawwakin wasu mutane yayin da su ka fita sintiri a Ogun
- Daga ciki akwai Azeez Ilias mai shekara 37 wanda Yarima ne na wani Basarake da ke kasar Ipokia
- An samu gawar Mista Azeez Ilias a cikin mota tare da wata mota mai suna Deborah a garin Idiroko
Ogun - Daily Post tace an tsinci gawar wani Bawan Allah mai suna Azeez Ilias da aka bayyana shi a matsayin ‘dan wani Sarki a kasar Ipokia, jihar Ogun.
Kamar yadda rahoton ya bayyana, an samu gawar Mista Azeez Ilias mai shekara 37 da haihuwa tare da wata mai suna Deborah a cikin wata mota.
Punch tace an samu gawar wadannan mutane ne a mota kirar Toyota Camry, a gaban wani gida a unguwar Ago Egun, karamar hukumar Idiroko, Ogun.
Yayin da aka iske gawar mutanen tsirara, ana kyautata zaton cewa motar da aka same su a mace a ciki, ta Marigayi Ilias ce, wanda mahaifinsa Basarake ne.
Rahoton na PUNCH Metro yace an samu kayan da ke jikin Ilias a wata kwata a gaban gidan Deborah, wanda aka samu gawarsu tare a farkon makon nan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jami’an tsaron So-Safe Corpes na Idiroko a Ogun, sun tabbatar da aukuwar wannan lamari, suka ce an samu gawawwakin ne da karfe 2:00 na safiyar Litinin.
Mai magana da yawun bakin dakarun So-Safe Corpes, Moruf Yusuf, ya fitar da jawabi, yace sun samu gawawwakin ne yayin da suka fita sintirin cikin dare.
Da yake bada karin bayani a ranar Talata, Yusuf, yace motar da aka samu gawawwakin ta na da launin toka ne, ya kuma bada lambar motar da LND 223 BV.
Sanarwar da ta fito daga bakin So-Safe Corpes a ranar Talata ta yaba da irin hadin-kan da ake samu tsakanin dakarunsu da jami’an ‘yan sanda na jihar Ogun.
Kakakin ‘yan sanda na Ogun, Abimbola Oyeyemi, yace bincike zai bayyana asalin abin da ya faru, yace zuwa yanzu ba a san dalilin mutuwar mutanen biyu ba.
Rahotanni marasa dadi su na zuwa mana cewa ‘yan bindiga sun hallaka daya daga cikin ‘yan majalisar dokokin Kaduna a makon nan, Hon. Rilwan Gadagau.
Hakan na zuwa ne bayan kwanaki an ji ‘yan bindiga sun harbe mutane a hanyar Kaduna-Zaria. Hon. Gadagau ya na cikin wadanda suka mutu a sanadiyyar harin.
Asali: Legit.ng