Dangote da jerin mashahuran masu kudin Afrika 5 da suke cikin Attajiran Duniya a 2021
A wannan rahoto, mun shiga babin Attajirai, inda muka tattaro maku jerin fitattun masu kudin nahiyar.
Bayan Aliko Dangote a yau, akwai wasu Attajiran nahiyar da suke cikin manyan masu kudi na Duniya.
An yi shekaru fiye da goma, ba a samu wani 'dan kasuwa da ya kama hanyar shan gaban Dangote ba.
Africa Business Insider ta kawo sunayen wadanda suka fi kowa arziki a Afrika. Hakan na zuwa ne a lokacin da Attajirin Duniya Elon Musk ya tafka asara.
Babban mai kudin Najeriya, Aliko Dangote ne na 102 a cikin jerin masu kudin Duniya. ‘Dan kasuwan ya motsa a jeringiyar Bloomberg Billionaires Index.
A Nuwamban 2021, mutanen Afrika biyar ne kacal a cikin manyan Attajirai 500 da ake ji da su.
Legit.ng ta kawo sunayen wadannan masu kudi:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
1. Aliko Dangote (Najeriya) - $19.2b
Aliko Dangote ya dade a matsayin mai kudin Afrika, ana hasashen ya mallaki akalla Dala biliyan 19.2. Dangote ya yi arziki ne da siminti, sukari, mai da kayan abinci.
2. Johann Rupert da danginsa (Afrika ta kudu) - $10.6b
Johann Rupert shi ne na 234 a jerin, ratarsa da Dangote tana da yawa ($9.2b). Rupert da danginsa ne suke da kamfanonin Jaeger-LeCoultre, Remgro da sauransu.
3. Natie Kirsh (Afrika ta Kudu) – $8.27b
A jerin Attajiran Duniya, Natie Kirsh mai $8.2b ya zo na 328. Kirsh yana da hannun jari a Jetro Holdings, sannan yana da gidajen abinci jihohi akalla 30 a Amurka.
4. Nicky Oppenheimer (Afrika ta Kudu) – $8.05b
Kamar Kirsh da Johann Rupert, shi ma Nicky Oppenheimer mutumin Afrika ta Kudu ne. Oppenheimer ne na 346 a jerin, ya na da akalla fam Dala biliyan 8.05.
5. Nassef Sawiris (Egypt) - $7.06b
Wanda aka rufe jerin da shi shi ne Nassef Sawiris da ake hasashen yana da fiye da Dala biliyan bakwai. Bamisren ya yi arziki ne da kamfanin taki na kasar Nederland.
Attajiran asali a Najeriya
A wani rahoto da muka kawo a makon da ya wuce, kun ga jerin wasu daga cikin attajiran farko da aka yi a Najeriya da yadda suka mallaki tarin dukiyarsu a tarihi.
Jerin ya na dauke da attajirin Arewa Alhaji Alhassan Dantata da irinsu Louis Odumegwu-Ojukwu wanda ya yi kudi ta hanyar shigo da kaya daga kasashen waje.
Asali: Legit.ng