Dantata, Ojukwu, Da Rochas da sauran masu kudin da suka shahara kafin samun ‘yancin-kai
- Tun fil azal, akwai manyan masu kudi a Najeriya wanda labarin dukiyarsu ya tsallaka kasashe.
- Legit.ng ta tattaro maku wasu daga cikin Attajiran farko da aka yi tun zamanin mulkin mallaka.
- Zuri’ar Alhassan Dantata da Odumegwu-Ojukwu sun yi kudin tun kafin Najeriya ta samu ‘yanci.
Wasu daga cikin masu kudin farko da aka fara yi a tarihi:
1. Candido Da Rocha (1860 – 1959)
Masana suna ganin Candido Da Rocha ne attajirin farko da aka yi, wanda ya mallaki miliyan a Najeriya. Da Rocha ya yi bauta a kasar Brazikl kafin ya zo Najeriya inda ya kafa daular kasuwanci.
Da Rocha ne ya jawo ruwan fanfo a wasu yaunkunan Legas irisu Iju, Yaba, da Ebute Metta.
2. Alhassan Dantata (1877 –1955)
Ba zai yiwu ayi batun dukiya ba tare da an kawo maganar gidan Alhasawa ba. Tun 1929 Dantata ya bada ajiyar kudi a bisa rakuma 20 a sabon bankin Bank of West Africa da aka bude a Kano.
Punch tace Alhassan Dantata ya yi kasuwancin gyada, goro, hatsi da dabbobi a kasashen Duniya.
3. Timothy Odutola (1902-1995)
Timothy Odutola shi ne shugaban kungiyar Manufacturers Association of Nigeria (MAN) na farko a tarihi. Tun kafin Najeriya ta samu ‘yanci daga hannun Ingila, Odutola ya zama babban mai kudi.
4. Sir Mobolaji Bank-Anthony (1907 - 1991)
Mobolaji Bank-Anthony ya rike shugaban kungiyar kasuwar hada-hadar hannun jari na kasa, ya na cikin masu hannun jari a Aero Contractors, kuma shi ya bude bankin M. de Bank Brothers
A shekarar 1931, Mobolaji Bank-Anthony ya fara zuwa Jamus da Ingila domin koyon kasuwanci.
5. Sir Louis Odumegwu-Ojukwu (1908 -1966)
Ana cewa Louis Odumegwu-Ojukwu ne mutumin da ya fara mallakar Biliyan a Najeriya. Baya ga haka mahaifin na Chuwkumeka Ojukwu ne ya fara rike kungiyar hada-hadar hannun jari.
Ojukwu ya yi arziki ne ta hanyar shigo da busasshen kifi da tufafi da harkar siminti a Najeriya.
An sace kudin 'yan fansho
Kun ji labarin yadda wasu manyan bankuna 2 suka taimakawa Abdulrasheed Maina ya sacewa ‘Yan fasho Naira Biliyan 2 a Najeriya. A karshe aka daure shi a kurkuku.
Alkalin kotun tarayya da ya zartar da hukuncin yace wadannan bankunan suna sane aka sace kudin Bayin Allah. Saura kiris a karbewa bankunan biyu laisin aikinsu.
Asali: Legit.ng