‘Yan Sanda za su biya N50m ga iyalin wani Bawan Allah da dakarun SARS suka kashe da zalunci

‘Yan Sanda za su biya N50m ga iyalin wani Bawan Allah da dakarun SARS suka kashe da zalunci

  • An zo karshen shari’ar da ake yi tsakanin Abba Hikima esq. da ‘yan sanda a kan kisan wani matashi.
  • Lauyan mai kare hakkin Bil Adama yace ya yi nasara a kan ‘Yan Sandan jihar Kano a gaban kotu.
  • Alkali ya kama ‘yan sanda da laifin da ake zarginsu, ya umarci su biya iyalin marigayin Miliyan 50.

Kano - Alkalin wani babban kotu da ke jihar Kano, Y.M. Ubale, ya bada umarnin ‘yan sanda su biya diyya ga iyalin Marigayi Mustapha Idris Muhammad.

Jami’an SARS da aka ruguza ake zargin sun kashe wannan mutum yana shekara 28, Mustapha Idris Muhammad. Hakan ya sa aka shigar da kara a kotun.

A shekarar 2019 wani matashin lauya mai kare hakkin Bil Adama a Najeriya, Abba Hikima ya kai karar jami’an ‘yan sandan zuwa kotu, yana neman hakkinsa.

Kara karanta wannan

Kwamitin da yake bincike a kan rikicin EndSARS yace dole a kawo Abba Kyari gabansa

Abba Hikima ya roki kotu tace kwamishinan ‘yan sanda na Kano, Uba Bangajiya da jami’in da ya yi bincike, Garba Galadima, su biya ‘yanuwan Marigayin N100m.

Shari'a ta zo karshe - Lauya

Lauyan ya bayyana wannan a shafinsa na Facebook, ya kuma ce ya yi nasara Alkali ya ba su gaskiya bayan tsawon sama da shekaru biyu ana ta shari'a.

‘Yan Sanda
Lauyan da ya kai karar 'Yan Sanda, Abba Hikima Hoto: @hikimaman
Asali: Facebook

A cewar lauyan, dakarun SARS sun azabtar da Mustapha Idris Muhammad har ya mutu, amma ‘yan sanda suka boye labarin mutuwarsa ga ‘yanuwan na sa.

‘Yan sandan jihar Kano sun cigaba da karbar kudi da abinci daga hannun ‘yanuwan wannan Bawan Allah na tsawon kwanaki 14 bayan ya mutu a hannunsu.

Hakan ya sa Lauyan ya nemi a kama ‘yan sanda da laifin kashe Muhammad babu gaira babu dalili wanda hakan laifi ne a sassa na 33 da 34 na tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Majalisa ta kawo dabarar hana magudin zabe, za a rika aiki da na’ura wajen tattara kuri’u

'Yan sanda sun yi mana karya - 'Danuwan mamacin

Daily Nigerian tace wani ‘danuwan mamacin, Abdulkarim Muhammad, ya shaidawa kotu cewa ba a sanar da su labarin mutuwar Mustapha Idris Muhammad ba.

Muhammad yace sai bayan makonni biyu suka san ‘danuwansu ya mutu, kuma ‘yan sanda sun kawo takardun karya domin su nuna ciwon ciki ne ya kashe shi.

Rahoton yace mai shari’a Y. M Ubale ya karbi korafai takwas na lauyan, ya bukaci a biya N50m ga iyalinsa wadanda aka hana suyi wa ‘danuwansu sutura da wuri.

EFCC tana shari'a da tsohon Minista

A makon nan aka ji EFCC ta koma kotu da Alhaji Abdu Bulama da wasu mutane hudu a jihar Yobe. Abdu Bulama ya taba rike kujerar Minnistan kimiyya da fasaha.

Ana zargin wadannan Bayin Allah da karbar N450m a hannun tsohuwar Minista, Diezani Alison-Madukwe da nufin taimakawa Goodluck Jonathan a zaben 2015.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng