Latest
Tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Danjuma Goje ya raba keken dinki da Naira miliyan 14 ga mutane 700 a mazabarsa ta Gombe ta Tsakiya a ranar Laraba.
Jam'iyyar APC ta amince yankin Arewa maso Yamma ya ci gaba da shugabancin jam'iyya mai mulki, hakan ya ƙara tabbatar da Abdullahi Ganduje a kujerarsa.
Hukumar fasaha da kere kere ta NASENI ta ce ana daf da kammala samar da jirgin sama na farko a Najeriya. NASENI ta ce jirgin Najeriya zai fara tashi sama.
Ministan ayyuka na Najeriya, Dave Umahi ya buƙaci masana'antun siminti su rage farashin kayansu daga N9,500 zuwa N7,000, ya kafa hujja da cewa dala ta karye.
Yayin da ake kokawa kan halin walwalar sojoji, Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar-janar Olufemi Oluyede, ya ƙara kuɗin ciyarwa daga N1,500 zuwa N3,000 a kullum.
Wasu tsagerun 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun hallaka jami'an 'yan sanda. 'Yan sandan sun rasu ne yayin wani artabu da suka yi.
Kamfanin Dangote Refinery ya sake rage farashin fetur daga ₦890 zuwa ₦825 kowace lita inda aka tabbatar da cewa a Lagos za a siyar da lita kan ₦860.
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da tsaurara matakan tsaro a kewayen karamar fadar sarkin Kano da ke Nasarawa, wurin da Aminu Ado Bayero ke zaune a ciki.
Bashir Ahmad, tsohon hadimin Muhammadu Buhari ya magantu kan salon mulkin dattijon daga shekarar 2015 zuwa 2023 inda ya ce ya dara Obasanjo, Yar'Adua da Jonathan.
Masu zafi
Samu kari