Latest
Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da kai hari masallacin kauyen Unguwan Mantau da ke yankin karamar hukumar Malumfashi a Katsina, an kashe mutane 13.
Najeriya ta ce tana shirye domin mayarwa Amurka martani kan dokokin biza da ta sanya wa 'yan kasar ta. Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya za ta dauki mataki.
Bayan ta da jijiyoyin wuya kan ganin yan sanda a Kano suna taimakawa dan siyasa rabon kuɗi ga jama'a, rundunar ta tabbatar da ɗaukar matakin ladabtarwa kan jami’an.
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Mathias Tsado, ya bi sahun masu son ganin Goodluck Jonathan, ya tsaya takara a zaben shekarar 2027 da ake tunkara.
Tinubu ya rage kuɗin wanke ƙoda zuwa ₦12,000 daga ₦50,000 a asibitocin tarayya, amma jama’a sun ce marasa lafiya na buƙatar jinya akai-akai da ya fi ƙarfin talaka.
Gwamnatin tarayya za ta rabawa talakawa tallafin kudi a gidaje miliyan 2.2. Karamin ministan jin kai, Tanko Sanunu ne ya bayyana hakan a wani taro a Abuja.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gudanar da zabukan cike gurbi. Jam'iyyar APC ta samu nasara a mafi yawan mazabun da aka gudanar da zaben.
Gwamnatin jihar Benuwai ta mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayi mai ba gwamna shawara kan harkokin hulda da jama'a da siyasa, Mary Yisa, wacce ta rasu.
Mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Martins Vincent Otse da aka fi sani da VDM ya jagoranci hana motocin Dangote wucewa da rana a jihar Edo saboda jawo hadura.
Masu zafi
Samu kari