
Latest







Kungiyar kwadago ta ce yunwa ta fara haifar da cututtuka kama su kwashoko a Najeriya. NLC ya ce akwai bukatar fitar da tare tsaren kawo saukin rayuwa.

Rahotannin sun nuna cewa da tsakar dare wayewar garin yau Litinin, wasu miyagun ƴan bindiga suka kashe mutum biyu a Abeokuta, babbar birnin jihar Ogun.

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta shiga tsakani domin kawo karshen dambarwar da ke tsakanin kungiyar kwadago da kamfanin wutar lantarki.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sauka a birnin Riyadh da ke Saudiyya domin halartar taron Larabawa da kasashen Musulunci inda za a tattauna muhimman batutuwa.

An fara shirye-shiryen gudanar da jana'izar tsohon shugaban hafsan sojojin kasan Najeriya (COAS), Taoreed Abiodun Lagbaja. Za a binne marigayin a Abuja.

Fasto Umo Eno, gwamnan jihar Akwa Ibom ya ba da tabbacin cewa zai biya ma’aikatan jihar albashi biyu a watan Disamba domin inganta bukukuwan Kirsimeti.

Gwamnatin jihar Kebbi ta tura tawaga wajen hafsun tsaron Najeriya domin hada kai wajen yaki da Lakurawa. Hafsun tsaro ya tabbatar da cewa za su yaki Lakurawa.

Gwamnatin jihar Kwara ta bayyana shirinta na rike albashi da alawus alawus na ma'aikatan da ba su mallakin lamɓar zama cikakken mazaunin jiha ba.

Dan wasan gaba na Super Eagles Ademola Lookman ya samu kuri’u daga kasashe 17 inda ya zo na 14 a neman lashe kambun Ballon d’Or na 2024 da maki 82.
Masu zafi
Samu kari