Latest
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yabawa Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo bisa nagartacceɓ shugabancin da ya ke yi wanda ya zama abin koyi ga ƴan ƙasa.
Bayan Shugaba Bola Tinubu ya sauya taken Najeriya, kungiyar lauyoyi ta ALDRAP ta shirya maka shugaban a kotu kan rashin bin tsari wurin tabbatar da dokar.
Wata kungiya mai rajin inganta harkokin shari'a a majalisa ta Association of Legislative Drafting and Advocacy Practitioners za ta maka shugaba Tinubu kotu.
Wata kotu dake zamanta a Koriya ta kudu ta umarci shugaban rukunin kamfanonin SK, Chey Tae-won ya biya tsohuwar matarsa Roh So-young won tiriliyan 1.38.
'Yan bindiga sun kai hare-hare a kauyukan jihar Katsina inda suka hallaka mutum 17. 'Yan bindigan sun kai hare-haren ne a kauyukan karamar hukumar Kankara.
Hakimai da sauran dagatai daga kauyukansu da kuma shugabannin riko na kananan hukumomi 44 sun kai caffan ban girma ne ga Sarkin a yau Juma'a a fadarsa.
Gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasiru Idris Kauran Gwandu ya naɗa sabbin sarakuna a jihar Kebbi da suka kunshi hakimai da magajin gari a kauyuka biyar.
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya soke daukar ma'aikata 10,000 da Nyesom Wike ya yi a karshen mulkinsa inda ya zargi rashin bin tsari a daukar ma'aikatan.
Manyan kungiyoyin kwadago a Najeriya sun ayyana fara yajin aiki daga ranar Litinin mai zuwa kan gazawar gwamnati a batun mafi ƙarancin albashi da kuɗin wuta.
Masu zafi
Samu kari