Latest
Sanatan da ke wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya ba gwamnati shawarar abin da ya kamata ta yi wa yaran da aka saki bayan an tsare su saboda zanga-zanga.
Wani jami’in hukumar tsaron farar hula (NSCDC) da aka karawa girma mai suna Muhammed Opatola da ke aiki da sashin Iwo ya fadi ya mutu bayan ya karbi albashi.
Wata motar haya da ta kuccewa direba ta daki bakin gada, ta faɗa kogi a karamar hukumar Njaba da ke jihar Imo, duka fasinjojin cikin motar sun kwanta dama.
Wasu 'yan kungiyar asiri na ci gaba da yakar juna a birnin Makurdi, babban birnin jihar Benue. Fadan ya jawo an samu asarar rayukan mutane tare da dukiyoyi.
Rundunar ƴan sanda reshen jihar Imo ta tabbatar da fashewar bom a kasuwar Orlu ta ƙasa da ƙasa da ke jihar Imo, ta ce miyagu 2 da suka dasa shi sun mutu.
Wata babbar kotun jihar Kano ta ba da umarni ga hukumomin gwamnatin tarayya kan yiwuwar hana ba kananan hukumomin Kano kudade daga asusun tarayya duk wata.
Kungiyar makarantu masu zaman kansu ta yi alkawarin ɗaukar nauyin karatun yaran zanga zanga da aka kama. Ta yi alkawari wa yaran ne bayan an sake su.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna godiyarsa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan sakin yaran da aka tsare saboda zanga-zangar da aka yi a Agusta.
Sabuwar kungiyar yan ta'adda mai suna Lakurawa ta ɓulla jihar Sokoto inda ta fara raba miliyoyi domin daukar matasa. Yan ta'addar na daukar matasa a N1m.
Masu zafi
Samu kari