Latest
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi magana kan zanga-zangar da ake yi a fadin kasar nan. Ya ce ya kamata gwamnonin Arewa su farka su yi abin da ya dace.
Majalisar Wakilai ta yi magana kan jita-jitar da ake yadawa na baraka tsakanin Shugabanta, Hon. Tajudden Abbas da mataimakinsa, Hon. Benjamin Kalu.
Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta fusata kan samamen da jami'an tsaro suka kai a hedkwatarta da ke birnin tarayya Abuja. Ta ce hakan abin kunya ne.
Wasu mabarata a Kano sun roki jagororin da su ka shirya zanga-zanga su yi hakuri, su janye saboda su samu damar fitowa neman na kai wa bakunansu.
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya ce tsare-tsaren Bola Tinubu a Najeriya su suka jefa al'umma cikin mawuyacin hali inda ya bukaci ya sauya salo.
An samu bambancin furuci tsakanin hukumomin tsaron kasar nan a kan harba bindiga yayin zanga-zangar lumana da matasan kasar nan ke gudanarwa saboda tsadar rayuwa.
Malamin addini kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a APC Tunde Bakare ya yi kira ga yan siyasa kan bukatar talakawa, ya ce ba wanda ya dauki nauyin zang zanga.
Gwamnatin Malam Sani ta sassauya dokar hana zirga-zirga da ta sanya a cikin garin Kaduna da Zariya, ta amince mutane su fita daga 8 na safe zuwa 6 na yamma.
Dan majalisar wakilai Uchenna Harris Okonkwo ya yi kira ga Bola Tinubu kan shawo kan damuwar talakawa maimakon yin magana kawai, ya ce ana wahalar rayuwa.
Masu zafi
Samu kari