Latest
Shugaba kuma jagoran matasa a tafiyar Kwankwasiyya, Abdulrahaman Mai Kadama ya fice daga tafiyar Abba Kabir Yusuf, ya ajiye mukaminsa zuwa APC a Kano.
Dele Alake, ministan ma’adanai, ya dage cewa an yi zanga-zangar nuna adawa da wahalhalun da ake yi a wasu garuruwa da nufin hambarar da gwamnatin Bola Tinubu.
Gwamnatin tarayya ta shawarci masu son a canza gwamnati a kasar nan da su jira har sai lokacin zaben 2027. Dele Alake ne ya ba da wannan shawarar.
Rukunin kamfanonin Dangote ya fitar da sanarwa kan rahoton cewa matatar man Dangote ta kayyade farashin litar fetur. Kamfanin ya ce ikirarin IPMAN ba gaskiya ba ne.
Tsofaffin shugabannin Najeriya, Muhammadu Buhari, Goodluck Jonathan da sauransu sun yiwa Shugaba Bola Tinubu alkalanci bayan ya shafe wata 14 yana mulki.
Kungiyar kafafen yada labaran Arewa (NBMOA) ta shigar da kara kan tashar talabijin ta Arewa24 gaban hukumomi bisa zargin bata al'adun al'ummar Hausawa.
Matatun man fetur suna da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin duniya. Akwai matatun mai guda 825 da ke aiki. Ga jerin guda 10 da suka fi girma.
Hukumar tattara kudaden shiga da kasafin kudi (RMAFC) ta yiwa Sanata Shehu Sani martani kan albashin sanatoci. RMAFC ta jero kudaden da ake turawa 'yan majalisar.
Sanata Muhammad Ɗanjuma Goje ya yi nasara, kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta tabbatar da shi ɗan APC, ta ci tarar jam'iyya mai mulkin jihar Gombe N200,000.
Masu zafi
Samu kari