Latest
Kotun Koli ta umarci ba kansiloli da shugabannin kananan hukumomi a Najeriya wa'adin shekaru hudu kamar yadda gwamnonin jihohi ke yi a tsarin mulki.
Yayin da ake cikin wani irin mayuwacin hali a Najeriya, an gudanar da addu'o'i da karatuttukan Alkur'ani mai girma domin neman mafita a jihar Kano.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi gargadi kan yunkurin da ake yi na durkusar da matatar man Dangote.
Jam'iyyar APC reshen jihar Kano, ta buƙaci a gudanar da bincike kan zargin karkatar da shinkafar gwamnatin tarayya a Kano. Ta zargi wasu jami'an gwamnati.
Malam Uba Sani ya ce gwamnatinsa ba za ta sake lamuntar a maimaita abin da ya faru ranar 1 da 5 ga watan Agusta, 2024 ba, ya haramta manyan taruka.
Shugaban cocin INRI Spiritual Evangelical Church, Primate Elijah Babatunde Ayodele, ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sallami Mele Kyari daga mukaminsa.
Gwamnatin jihar Adamawa ta tafka asara bayan matasa sun wawashe babbar mota makare da takin zamani a karamar hukumar Demsa da ke jihar a Najeriya.
Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Rijiyar Lemo ya gargadi 'yan kasuwa da masu hali su ji tsoron Allah wurin tausayawa talakawa saboda neman albarka.
Gwamnatin Poland ya buƙaci mahukuntan Najeriya su yi hakuri su sako ƴan kasarta bakwai da jami'an tsaro suka kama ds laifin ɗaga tutar Rasha a Kano.
Masu zafi
Samu kari