Sadiya Haruna, Rabi Isma'ila da wasu Jarumai Mata 2 da Kotu ta ɗaure a Kurkuku

Sadiya Haruna, Rabi Isma'ila da wasu Jarumai Mata 2 da Kotu ta ɗaure a Kurkuku

  • A kwanan nan ne wata Kotun Majistire dake jahar Kano ta ɗaure Jaruma Sadiya Haruna na tsawon watanni 6 a gidan Yari
  • Hakan yasa muka tattaro muku jerin Jaruman Fim mata a Najeriya da Kotu ta taɓa yanke musu hukunci ɗauri bayan kama su da laifi
  • Daga cikinsu, har da Jaruma Rabi Isma'il, wacce Kotu ta kama da laifin kashe saurayinta a jihar Kano

Jaruman shirin fim a Najeriya na jin rayuwa ta musu daɗi musamman lokacin da tauraruwarsu ke haskawa, to amma babu wanda ya fi ƙarfin doka.

Daily Trust ta rahoto cewa a baya-bayan nan Kotu ta ɗaure Jaruma a Kannywood, kuma mai ɗaukar hankali a kafafen sada Zumunta, Sadiya Haruna, a gidan Yari.

Gidan Yari
Sadiya Haruna, Rabi Isma'ila da wasu Jarumai Mata 2 da Kotu ta ɗaure a Kurkuku Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Mun tattaro muku jerin wasu Jarumai mata a Najeriya, waɗan da Kotu ta tura su gidan gyaran hali.

Kara karanta wannan

Bayan shekara 9, Kotu ta datse igiyoyin auren Sadiya Adamu saboda ta cika daukar zafi

1. Sadiya Haruna

Sunan Sadiya Haruna sananne ne a masana'antar shirya Fina-Finan Hausa Kannywood da kuma masu amfani da kafafen sada zumunta a arewacin Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaruma Sadiya mai yawan jawo cece-kuce ta fara suna ne yayin da ta fara fitowa a shirin fim mai suna, "Bakon Legas" a shekarar 2017, ta jima tana jefa kanta cikin rikici.

Kotun musulunci a Kano ta taɓa umartan Sadiya ta halarci Islamiyya na tsawon watanni shida bisa kama ta da laifin yaɗa abubuwan da suka shafi batsa a kafafenta na sada zumunta.

A shekarar 2021, aka kori jaruma Sadiya Haruna daga kasancewarta Mamba a masana'antar Kannywood.

A kwanan nan, Kotun Majistire a Kano ta ɗaure Sadiya na tsawon watanni shida bisa ɓata sunan tsohon mijinta a kafafen sada zumunta, inda ta kira shi da ɗan luwaɗi, da sauran su.

Kara karanta wannan

Gaskiya 6 da ya kamata ku sani game da Jaruma Sadiya Haruna da Kotu ta ɗaure

Jarumai Mata
Sadiya Haruna, Rabi Isma'ila da wasu Jarumai Mata 2 da Kotu ta ɗaure a Kurkuku Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

2. Rabi Isma'il

A shekarar 2002, wata babbar Kotu a jahar Kano ta yanke wa Jarumar Kannywood yar shekara 39, Rabi Isma'il, hukuncin kisa bisa kashe saurayinta.

Kotun ta kama jarumar da laifin yaudarar saurayinta, Ibrahim, zuwa yawon shaƙatawa a Tiga Dam dake Jahar Kano, ta sanya masa guba a Cakuleti kuma ta tura shi cikin ruwa.

Rabi ta tsere daga gidan Yari a watan Disamba, 2017, amma jami'an gidan Yari da taimakon hukumar DSS suka samu nasarar sake cafke ta.

An sake ɗaure Jarumar, wacce aka fi sani da Rabi Cecelia, a gidan gyaran hali a shekarar 2017.

3. Ibinabo Fiberesima

Ibinabo, jaruma ce a masana'antar Nollywood dake kudancin Najeriya kuma tsohuwar sarauniyar kyau. A 2009 aka gurfanar da ita da zargin salwantar da rayuwar wani mutum.

Haka nan kuma Kotu ta tuhume ta da tuƙin ganganci bayan ta yi kuskuren kashe wani mutumi, Giwa Suraj a shekarar 2006.

Kara karanta wannan

Sauya sheka: Bayanai sun fito kan tattaunawa tsakanin mataimakin shugaban kasa da Kwankwaso

A watan Maris, 2016, babbar kotun tarayya dake Legas ta ɗaure jarumar a gidan Kurkuku na tsawon shekara biyar, amma kotun ɗaukaka ƙara ta bada belin ta a watan Afrilu, 2016.

4. Taiwo Akinwande

Babbar Kotun tarayya dake zamanta a jahar Legas, ta yanke wa fitacciyar Jarumar Yarbawa, Taiwo Akinwande Hassanat, hukuncin zaman gidan kaso na shekara uku ko tarar Miliyan ɗaya.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ce ta gurfanar da jarumar a gaban kotu bisa zarginta da safarar miyagun kwayoyi, kuma ta amince da laifinta.

A wani labarin kuma Jaruma Sadiya Kabala ta bayyana yadda mutane ke kokarin ganin bayan matan Kannywood dake kasuwanci

Jarumar Kannywood, Sadiya Kabala, ta koka kan yadda mutane ke da taurin bashi idan ka amince ka ba su kayan ka.

Jarumar tace da kasuwanci ne suke samu suna tsira da mutuncin su, musamman idan suka daina harkar shirin fim.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262