Labaran duniya
Yayin da ake yada faifan biyidon Bola Tinubu a South Africa, fadar shugaban kasar Najeriya, ta musanta abin da ake yadawa inda ta bayyana yadda abin ya faru.
Yayin da ake ci gaba da aikin hajji, Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya sake abin alheri ga maniyyatan jihar da ke kasar Saudiyya da kyautar riyal 100.
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya koka kan yadda alhazai suka tsinci kansu a Saudiyya a bana inda ya caccaki tsare-tsaren hukumar alhazai ta NAHCON.
Amurka ta janye sojojinta da suka kafa sansani a Nijar domin yakar ta'addanci biyo bayan wa'adin da sojojin da suka yiwa Muhammad Bazoum juyin mulki suka bayar.
Hukumomi sun bayyana kame wasu mutum 18 da aka ce mahajjatan bogi ne a daidai lokacin da suke shirin shiga birnin Saudiyya ana kwana biyu Arfa a kasar.
Al'ummar musulmi sun kammala isa kasa mai tsarki yayin da a yau za a fara gudanar da aikin hajjin bana. Sai dai harin Isra'ila a a Gaza ya hana su zuwa Saudiyya.
Hukumar sojojin Najeriya ta tabbatar da aniyarta na tura dakaru kasar Gambia domin taimaka mata wurin wanzar da zaman lafiya da kare lafiyar al'umma.
Bankin duniya ya gargadi gwamnatin Najeriya kan karin kudin ruwa da ake yi ga masu karbar bashi. Bankin ya ce karin kudin zai kara kawo tashin farashin kayayyaki.
Senegal ta shiga sahun kasashe masu arzikin man fetur bayan da kamfanin Woodside Energy na Australiya ya sanar da fara aikin hakar man a kasar da ke yammacin Afirka.
Labaran duniya
Samu kari