Amurka Ta Gabatar da 'Tayi na Karshe Mafi Kyau' ga Tawagar Iran a Teburin Tattaunawa
- An kammala zagaye biyu na tattaunawa tsakanin Amurka da Iran a birnin Islamabad na kasar Pakistan amma ba a cimma matsaya ta karshe ba
- Mataimakin shugaban kasar Amurka, JD Vance ya yi takaitaccen bayanin yadda zaman ya kaya da kuma halin da ake ciki
- Vance, jagoran tawagar Amurka ya ce kasarsa ta gabatar da tayi mafi kyau kuma na karshe ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Pakistan - Mataimakin shugaban kasar Amurka, JD Vance, ya yi takaitaccen jawabi ga manema labarai jim kadan bayan fitowa daga zauren tattaunawa da Iran a birnin Islamabad.
Vance ya bayyana cewa tawagar Amurka ta rika tuntubar Shugaba Donald Trump akai-akai a duk tsawon lokacin da aka shafe ana tattaunawar, wacce ta dauki tsawon zagaye biyu.

Source: Getty Images
Amurka ta gabatar da tayin karshe ga Iran

Kara karanta wannan
Bayan gama zagayen farko, an bayyana bukata 1 da Amurka ta amince za ta yi wa Iran
Tashar Al-Jazeera ta rahoto mataimakin shugaban kasar na cewa Amurka ta gabatar da tayi na karshe kuma wanda take ganin shi ne mafi kyau ga wakilan Iran.
“Mun rika kiran shugaban kasa a kowane lokaci. Ban san sau nawa muka yi magana da shi ba, ko sau shida ne, ko sau goma sha biyu a cikin sa’o’i 21 da suka gabata.
“Mun fara tattaunawar ne da kyakkyawar niyya kuma mun bar nan da wata shawara mai sauki, wata hanyar fahimta wadda ita ce tayin mu na karshe kuma mafi kyau. Za mu gani ko Iraniyawa za su amince da shi.”
- JD Vance.
Wadanne batutuwa suka tatttauna a taron?
Mataimakin shugaban kasar Amurka ya ce bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da dama, amma dai ba a kai ga cimma yarjejeniya ta karshe ba.
Vance ya ci gaba da cewa:
“Mun kasa kaiwa ga matsayin da Iraniyawa za su amince da sharuddanmu. Ina ganin mun nuna sassauci sosai; kuma mun yi kokarin tafi da su yadda ya kamata."
“Shugaban kasa ya gaya mana cewa, dole ne mu zo nan da kyakkyawar niyya kuma mu yi kokari iya iyawarmu domin ganin an cimma yarjejeniya. Mun yi hakan, amma abin takaici, ba mu iya samun wani ci gaba ba.”

Source: Twitter
Babban abin da Amurka ta nema
Lokacin da aka tambaye shi game da abin da Iraniyawa suka ki amincewa da shi, mataimakin shugaban kasar ya ce ba zai shiga cikin cikakkun bayanai ba.
Sai dai ya bayyana Amurka tana neman tabbacin cewa Iran ba za ta nemi mallakar makamin nukiliya ba, kamar yadda The Cable ta rahoto.
“Gaskiyar lamarin ita ce, muna bukatar gani a aikace cewa ba za su nemi mallakar makamin nukiliya ba, kuma ba za su nemi kayan aikin da za su ba su damar kera makamin nukiliya cikin sauri ba.
"Wannan shi ne babban burin shugaban Amurka, kuma abin da muka yi kokarin cimmawa ke nan ta wadannan tattaunawar,” in ji shi.
A wani rahoton, kun ji cewa
Asali: Legit.ng
