Bayan Gama Zagayen Farko, An Bayyana Bukata 1 da Amurka Ta Amince Za Ta Yi Wa Iran
- Amurka ta amince ta saki wasu kadarorin kasar Iran, lamarin da ya kara karfafa gwiwar kasar wajen ci gaba da tattaunawa a Pakistan
- Wata majiya da ke kusa da tawagar Iran a Islamabad ta ce Amurka ta kuma amince za ta umarci Isra'ila ta rage hare-hare a Lebanon
- Bayanai sun nuna cewa an kammala zagayen farko na tattaunawa, wacce aka kira da mafi sirri idan aka kwatanta da na baya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Rahotanni daga tawagar Iran sun bayyana cewa kasar Musulunci ta amince ta koma teburin tattaunawar sulhu ne bayan Amurka ta yarda ta saki wasu kadarorin Iran da aka rike.
Wannan na daga cikin muhimman bukatun da Iran ta gabatar a cikin sharudda 10 da ta shimfida gabanin tsagaita wuta a yakin Gabas ta Tsakiya.

Source: Getty Images
Sai dai har yanzu Amurka ba ta tabbatar da wannan mataki a hukumance ba, kamar yadda tashar Al-Jazeera ta ruwaito.
Rage hare-hare a Lebanon
Rahotanni sun kuma nuna cewa bayan haka, Iran ta samu wani irin tabbaci daga Amurka cewa Isra’ila za ta rage kai hare-hare a Lebanon.
Haka kuma wasu kafofin yada labarai na Iran sun ruwaito cewa Amurka za ta saki kudaden Iran da aka rike.
Sai dai babu wani tabbaci daga bangaren Amurka ko Isra’ila dangane da wannan batu, duk da cewa an samu raguwar hare-hare a Beirut da yankunan kudancin Lebanon.
Iran na tsaka mai wuya kan Lebanon
A halin yanzu, Iran na cikin wani yanayi mai sarkakiya, inda a bangare guda, ba ta son gaza kare kanta ko kuma alakarta da kungiyar Hezbollah ta Lebanon ba, domin hakan na da alaka da martabarta da tasirinta a yankin.
A bangare guda kuma, ba ta son rusa yarjejeniyar tsagaita wuta saboda wasu dalilai na waje, lamarin da ke kara jefa Iran cikin yanayi mai cike sarkakiya.
Bayanai sun nuna cewa an kammala zagayen farko na tattaunawa, wacce aka kira da mafi sirri idan aka kwatanta da na baya, saboda karancin bayanan da ke fita zuwa jama’a.

Source: Getty Images
Amurka da Iran sun ci gaba da tattaunawa
A halin yanzu, ana ci gaba da tattaunawa a otel din Serena da ke Islamabad, inda aka ruwaito cewa wakilan sun sake komawa wani zagaye domin ci gaba da tattaunawa a cikin dare.
Lokacin da aka tattara wannan rahoto, karfe 11 na dare ne a Islamabad, kuma babu alamar cewa bangarorin za su tashi daga tattaunawar nan ba da jimawa ba.
A wani labarin, kun ji cewa
Asali: Legit.ng

