An Kammala Tattaunawa Ta Farko, An Ji Yadda Ta Kaya tsakanin Amurka da Kasar Iran
- Amurka da Iran sun kammala mataki na farko na tattaunawar sulhu, wanda ya gudana a birnin Islamabad na kasar Pakistan yau Asabar
- Wakilan kasashen biyu sun dauki dogon lokaci suna tattaunawa, sun ci abinci tare duk a kokarin lalubo hanyar tabbatar da zaman lafiya
- Wata majiya ta ce Pakistan na kokarin ganin an kara wa’adin tattaunawar da akalla kwana guda domin a samu karin lokaci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Islamabad, Pakistan - Rahotanni daga majiyoyin da ke kusa da masu shiga tsakani sun tabbatar cewa an kammala matakin farko na tattaunawar kai tsaye tsakanin Amurka da Iran a Pakistan.
Majiyoyin sun ce a yanzu bangarorin biyu na musayar takardu a rubuce domin tabbatar da cewa sun fahimci juna kan yarjejeniyoyin da aka tattauna kansu a yau.

Source: Getty Images
Yadda tattaunawar Amurka da Iran ta gudana
Tashar Al-Jazeera ta tattaro cewa bayanan da ke fitowa daga birnin Islamabad sun nuna cewa an yi zagaye da dama na tattaunawa cikin yanayi mai kyau, inda wakilan Amurka da Iran suka tattauna cikin fahimta.
Bugu da kari, wakilan sun ci abinci tare, sannan suka ci gaba da musayar bayanai domin karfafa abin da aka tattauna.
Daga bangaren Jamhuriyar Musulunci ta Iran, an bayyana cewa wakilan kasar sun tattauna a tsakaninsu, kuma suna kokarin gano hanyoyin da za su kara matsa wa gaba wajen cimma yarjejeniya.
Pakistan na neman karin lokaci
Wata majiya ta ce Pakistan na kokarin ganin an kara wa’adin tattaunawar da akalla kwana guda domin a samu karin lokaci na tattaunawa tsakanin kasashen biyu.
Sai dai har zuwa yanzu ba a amince da hakan ba, amma majiyar ta ce gwamnatin Pakistan na kokarin shawo kan bangarorin.
Jami’an diflomasiyya na Pakistan sun ce har yanzu suna da fata, suna kokarin shawo kan bangarorin biyu su sassauta matsayinsu, kamar yadda NBC Hausa ta rahoto.
Amurka da Iran sun kama hanyar cimma matsaya?
Sai dai nasarar tattaunawar za ta dogara ne da yadda shugabannin bangarorin biyu watau kasar Amurka da Iran, za su yanke hukunci kan yadda za a ci gaba da wannan zama.

Source: Getty Images
A yau Asabar, 11 ga watan Afrilu, 2026 aka fara wannan tattaunawa tsakanin Amurka da Iran, bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a daren Talata, kuma ta fara aiki washe gari.
Bayanai daga tattaunawar da ta gudana yau ta nuna cewa kasashen biyu sun fara fahimtat juna duk da dai kowane ya kafa sharudda da ake bukatar tattake wuri a kansu.
Halin da jagoran Iran, Khamenei ke ciki
A wani rahoton, kun ji cewa jagoran addini na ƙasar Iran, Mojtaba Khamenei, yana ci gaba da murmurewa daga munanan raunuka da ya samu.
Mojtaba Khamenei yana murmurewa ne daga raunukan da ya samu a fuskarsa da kuma ƙafafunsa sakamakon harin sama da ya yi sanadin kisan mahaifinsa a farkon yaƙin.
Majiyoyin waɗanda suka nemi a sakaya sunayensu, sun ce jagoran mai shekaru 56 yana samun sauƙi kuma har yanzu tu nan insa yana nan garau.
Asali: Legit.ng

