Bayan Ta Sha Alwashin Kashe Netanyahu, Iran Ta Kai Farmaki Muhimman Cibiyoyi 2 a Isra'ila
- Dakarun sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun ci gaba da kai hare-hare kan muhimman wurare a kasar Isra'ila
- A wata sanarwa da suka fitar yau Asabar, 15 ga watan Maris, 2026, sojojin Iran sun ce sun harba makamai zuwa wasu cibiyoyin tsaron kasar ta Yahudawa
- Haka zalika wasu rahotanni sun nuna cewa Iran ta jikkata akalla mutane biyu a sababbin hare-haren da ta kai Isra'ila da safiyar yau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Israel - Dakarun sojojin Iran sun sanar da ci gaba da kai hare-hare da makamai masu linzami kan muhimman wurare a kasar Yahudawa watau Isra'ila.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna shakku kan halin da Firaministan Isra'ila ke ciki, wanda Iran ta sha alwashin cewa za ta faraute kuma ta tura shi lahira.

Source: Getty Images
Iran ta kai hari cibiyoyin tsaron Isra'ila
Tashar Al-Jazeera ta ruwaito cewa a wata sanarwa da sojojin Iran suka fitar yau Asabar, sun ce sun kai hare-hare da jirage marasa matuka kan muhimman cibiyoyin tsaron Isra'ila.
Sanarwar ta ce hare-haren sun nufi hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta Lahav 433 ta Isra'ila da kuma cibiyar sadarwar tauraron ɗan adam ta tsaro ta Gilat Satellite Communications Center.
Sai dai sojojin Iran ba su bayyana takamaiman biranen da suka kai hare-haren ba, haka kuma ba su fadi irin barnar da aka yi ba.
Rahoton jikkata mutane a Isra’ila
A gefe guda kuma, rahotanni daga Isra’ila sun ce mutane biyu masu shekaru kusan 50 sun samu ƙananan raunuka bayan wani sabon harin makamai masu linzami daga Iran.
Hukumar agajin gaggawa ta Isra’ila 'Magen David Adom' ta ce an jikkata mutanen ne sakamakon fashewar wani makami da ya fado yankinsu.

Kara karanta wannan
To fa: Musayar wutar da ake tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran ta shiga wani muhimmin mataki
The Times of Israel ta ruwaito cewa wani makami mai linzami da ke ɗauke da kananan bama-bamai ya tarwatse a birnin Eilat da ke kudancin Isra’ila da wasu sassan ƙasar
Hukumomin Eilat sun ce an harbo wannan makami tun kafin ya kai ga birnin ta hanyar tsarin kariyar sararin samaniya na Isra’ila.

Source: Getty Images
Haka zalika wasu rahotanni sun ce wasu makaman rokoki sun faɗa a cikin biranen: Bnei Brak da Ramat Gan, wadanda ke cikin babban yankin Tel Aviv.
‘Yan sandan Isra’ila sun ce suna binciken wurare da dama inda tarkacen makamai da rokoki suka faɗi.
Iran ta shirya koyawa Amurka darasi
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin kasar Iran ta sake jaddada shirinta na ci gaba da mayar da martani kan sansanonin sojojin Amurka da kasar Isra'ila.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sha alwashin koya wa kassshen Amurka da Isra'ila darasin da ba za su taba mantawa da shi ba a tarihi.
Ma'aikatar harkokin wajen Iran ce ta bayyana hakan, tana mai cewa dakarun sojojin kasar ta Musulumci sun shirya tunkarar kowane irin kalubale a wannan yaki da ke gudana.
Asali: Legit.ng
