Saudiyya Ta Fitar da Sanarwa ga Musulmi Kwanaki 2 kafin Fara Azumin Ramadan

Saudiyya Ta Fitar da Sanarwa ga Musulmi Kwanaki 2 kafin Fara Azumin Ramadan

  • Saudiyya ta buƙaci al'ummar musulmi su fara duba jinjirin watan Ramadan daga yammacin gobe Juma'a, 28 ga watan Fabrairu, 2025
  • A wata sanarwa da mahukuntan ƙasar suka fitar, sun bukaci duk wanda Allah ya sa ya ga watan ya kai rahoto ga kotu mafi kusa da shi
  • Idan aka ga watan ranar Juma'a, al'ummar musulmi a kasar Saudiyya za su tashi da azumi ranar Asabar, 1 ga watan Maris

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Riyadh, Saudiyya – Mahukuntan ƙasar Saudiyya sun bukaci al’ummar Musulmi su fara duban jinjirin watan Ramadan a daren Juma’a, 28 ga Fabrairu, 2025.

Ranar Juma'a watau gobe ta zo daidai da 29 ga Sha’aban, 1446H a kalandar watannin addinin Musulunci.

Duban wata a Saudiyya.
Kasar Saudiyya ta buƙaci Musulmi su fara duban jinjirin watan Ramadan Hoto: @insharifain
Asali: Twitter

Kotun ƙolin Saudiyya ta buƙaci ƴan ƙasar su duba jinjirin watan Ramadan gobe Juma'a a wata sanarwa da shafin Inside The Haramain ya wallafa a manhajar X.

Kara karanta wannan

Fara azumi: Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwa kan watan Ramadan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, an bukaci duk wanda ya yi tozali da jinjirin watan ya kai rahoto ga kotu mafi kusa don tabbatar da shigowar watan Ramadan.

Muhimmancin duban jinjirin wata

A kowace shekara, Musulmi a duniya na jiran sanarwa daga hukumomin addini domin sanin ranar da za a fara azumin watan Ramadan.

Kotun Koli ta Saudiyya ita ke da alhakin tabbatar da ganin watan kafin sanar da fara azumi a kasar mai tsarki.

Duban watan yana daga cikin alamomin shigowar watan Ramadan, wanda Musulmi ke gudanar da azumi na kwanaki 29 ko 30.

Wannan wata mai alfarma na da matukar muhimmanci a addinin Musulunci, domin ana yawaita ibada, sadaka da karatun Alkur’ani Mai Girma.

Ramadan: Za fara duban wata a Saudiyya

Kotun Koli ta bukaci mazauna Saudiyya da sauran Musulmi da ke kasar da su kasance cikin shiri domin duba jinjirin watan a daren gobe Juma'a.

Kara karanta wannan

Yaki da zaman kashe wando: Sanata Goje ya raba miliyoyi da kayayyaki

Sanarwar ta ce:

"Kotun kolin Saudiyya ta na kira ga 'yan kasa da mazauna da su fara duba jinjirin watan Ramadan a yammacin ranar Juma'a 28 ga watan Fabrairun 2025 daidai da 29 Sha'aban 1446H.
"Duk wanda ya ga jinjirin watan sai ya kai rahoto kotu mafi kusa."

A wasu kasashen Musulmi, ana amfani da hanyoyin zamani kamar tauraron dan adam da na’urorin hangen nesa don tabbatar da ganin sabon wata.

Sai dai a ƙasar Saudiyya da wasu kasashen Larabawa, an fi dogara da ido wajen hango watan amma duk da haka suna amfani da na'ororin hangen nesan.

Muhimmancin watan Ramadan

Ramadan wata ne na ibada da gafara, wanda Musulmi ke tsarkake kansu ta hanyar azumi, sallah, karatun Alkur’ani da ayyukan alheri.

Haka kuma, ana amfani da watan domin karfafa zumunci da taimakon marasa karfi.

Al’ummar Musulmi a duniya na jira sanarwar shugabanninsu domin tabbatar da ranar da za a fara azumi.

Kara karanta wannan

Jirgin sojoji ya faɗo kan gidajen mutane, Janar da wasu sama da 40 sun mutu

Ana sa ran cewa idan an ga jinjirin watan ranar Juma’a, za a fara azumin ranar Asabar, 1 ga Maris, 2025.

Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwa

A wani labarin, kun ji cewa sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abaubakar III ya buƙaci musulmin Najeriya su fara duban jaririn watan Ramadan ranar Juma'a.

Fadar Sarkin Musulmi ta bukaci wadanda suka ga watan a fadin Najeriya su tuntube ta ta wasu lambobin wayoyi da ta bayar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262