Sabon Nau'in Korona: Kimanin Mutum 60,000 Sun Mutu A Kasar China Cikin Makonni 5
- Gwamnatin kasar Sin ta sanar da adadin wadanda suka halaka sakamakon Korona kwanakin nan
- Cutar ta Korona na cigaba da sauya zani lokaci bayan lokaci kuma abin ya sake tsamari a Sin
- Yan kasar Sin sun gudanar da zanga-zangan bukatar cire dokokin kule da hana fitar don cutar
Kimanin mutum 60,000 suka rasa rayukansu a Kasar Sin tsakanin watan Disamba 2022 kawo yanzu sakamakon annobar cutar Korona da taki ci, taki cinyewa.
Dubunnan mutane sun kamu da sabon nau'in cutar ne bayan Shugaban kasar, Xi Jinping, ya sassauta dokar hana fita a watan, UK Guardian ta ruwaito.
Wani rahoton jami'ar Peking ya nuna cewa sama da yan kasar Sin milyan 900 sun kamu da cutar.
Rahoton yace mafi akasarin mazauna birane a kasar wanda alkalumansu ya kai 70%-90% sun kamu da cutar.
Hukumomi a kasar Sin sun sanar da cewa mutum 59,938 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shugabar sashen kiwon lafiya, Jiao Yahui, a ranar Asabar ta sanar da cewa akalla mutum 59,938 ne suka mutu tsakanin ranar 8 ga Disamba, da 12 ga Junairu, riwayar BBC.
Wannan ya hada da mutum 5,500 da suka mutu sakamakon rashin iya numfashi, sauran kuma sakamakon wasu cututtuka da suke fama da su gabanin kamuwa da Korona.
Jiao ta kara da cewa mafi akasarin wadanda suka mutu sun kai shekaru 80 a duniya.
Akwai Bukin Shekara-Shekara
Daga ranar 21 ga Junairu, akwai bukukuwan tunawa da yan gudun hijra mafi yawa a tarihin duniya da ake yi a Sin inda miliyoyin mutane kan yi tafiya kai ziyara.
Gwamnatin jihar ta shawarcesu kada su kai ziyara wajen yan'uwansu da suka tsufa saboda kada su shafa musu cutar.
Ta ce kawo ranar 23 ga Disamba, mutum milyan 2.9 ne suka kamu da cutar amma yanzu sun ragu zuwa 477,000. Ta bayyana hakan ranar Alhamis.
Babban Dan takarar Shugaban Kasa Ya Kamu Da Sabuwar Nauyin Korona
A gida Najeriya kuwa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Dumebi Kachikwu, ya sanar da cewa shima ya kamu da cutar Korona kuma ya killace kansa tuni.
Ya yi kira ga a bi a hankali wajen yin kamfe kada hannun agogo ya koma baya.
Asali: Legit.ng