Gwamnatin Amurka ta amince Buhari ya kashe $1bn domin shigo da wasu jiragen yaki

Gwamnatin Amurka ta amince Buhari ya kashe $1bn domin shigo da wasu jiragen yaki

  • Ana kokarin magance matsalar rashin tsaro da ake yawan fama da ita a wasu yankunan Najeriya
  • Ma’aikatar harkokin gidan kasar Amurka ta ba gwamnatin tarayya damar sayen wasu jiragen yaki
  • Gwamnatin Muhammadu Buhari za ta kashe $1bn a kan jirage masu barin wuta da horas da jami’ai

Abuja - Ma’aikatar harkokin gida na Amurka ta amincewa gwamnatin Najeriya sayen jiragen yaki masu saukar ungulu na 12 AH-1Z Cobra a kan kudi $1bn.

Wani rahoto da Punch ta fitar a ranar Juma’a ya nuna wannan kwangila za ta ci kusan $1b. A kudin Naira, za a kashe kimanin Naira biliyan 414.5 kenan.

A karshen makon nan hukumar Defense Security Cooperation Agency ta Amurka ta bada sanarwar yarjejeniyar da aka cin ma da sojojin na Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya ta fara rabon buhunan abinci kamar yadda Buhari ya bada umarni

Hakan na nufin majalisar Amurka ta janye takunkumin da ta kakabawa gwamnatin Najeriya na sayen makamai saboda zargin ana cin zarafin Bayin Allah.

Sojoji na cin zarafin jama'a

Rahoton YahooNews ya ce daga cikin wannan kudi, akwai Dala miliyan 25 da aka ware domin a horas da jami’an tsaro kan yadda za su kare hakkin Bil Adama.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jiragen da aka saya sun hada da Bell-made Cobras da wasu na’urori da ke dawo da makami mai linzafi kan saiti da kuma kayan yakin da ke aiki a cikin dare.

Buhari
Buhari ya kaddamar da jirgin sojoji Hoto: www.thisdaylive.com
Asali: UGC

Ina takunkumin da aka sa?

A shekarun da suka gabata wasu kwararrun Sanatoci da ke aiki a kwamitin hulda da kasashen Duniya suka dakatar da a saidawa Najeriya da kayan yaki.

Ana zargin sojojin kasar nan su ka keta alfarmar al'umma da sunan ana yaki da ta'addanci.

Kara karanta wannan

Wata uku da shiga 2022, majalisa ta amince da kasafin kudin 2022, za a ci bashin N965.42bn

Bob Menendez, ya shaidawa sakataren gwamnatin Amurka, Antony Blinken cewa akwai bukatar a duba takunkumin sayen makaman da aka sa wa Najeriya.

Wannan cinikin makamai zai taimakawa Najeriya wajen yin yaki ta sararin samaniya tare da kawo zaman lafiya da bunkasa alakar da ke tsakanin kasashen.

Rahoton ya ce Bob Menendez yana ganin akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta tashi tsaye a kan matsalar tsaro da ya dabaibaye wasu yankunan kasar nan yau.

‘Dan majalisar na New Jersey ya yi magana a game da ram da aka yi da Omoyele Sowore tun kwanaki.

Takarar Orji Kalu a 2023

An ji Sanata Orji Uzor Kalu ya cika baki cewa karfin tattalin arzikin Najeriya zai habaka tamkar na Amurka a cikin shekaru hudu muddin ya zama shugaban kasa.

A cewar Kalu baya ga samar da tsaro, karfn GDP na Najeriya zai zama tamkar na Amurka, Jafan da sauran manyan kasashen Duniya, idan har ya karbi mulki a 2023

Kara karanta wannan

ICPC ta fallasa Sanatocin Kebbi, Jigawa da Taraba da suka yi gaba da kudin talakawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng