Sojojin Ukraine sun hallaka wani Hafsun Sojan da kasar Rasha ta ke ji da shi a filin yaki
- An tabbatar da cewa Manjo Janar Vitaly Gerasimov ya kwanta dama a yankin gabashin kasar Ukraine
- Janar Vitaly Gerasimov da wasu sojojin na sa sun mutu ne a wajen yakin Rasha da kasar Ukraine
- Mutuwar babban sojan kasar ta na zuwa ne kwanaki kadan bayan an kashe Andrei Sukhovetsky
Ukraine - Rahotanni daga ketare sun tabbatar da mutuwar wani Janar na kasar Rasha a wajen yaki. Sojan ya mutu yana fada a garin Kharkiv, kasar Ukraine.
Jaridar The Guardian ta fitar da rahoto a makon nan inda aka ji cewa ma’aikatar tsaron kasar Ukraine ta tabbatar da mutuwar Manjo Janar Vitaly Gerasimov.
Ma’aikatar tsaron kasar ta Ukraine ta ce shugaban hafsun rundunar sojojin kasa na 41 na Rashan ya gamu da ajalinsa ne yayin da yake yaki a gabashin Ukraine.
Manjo Janar Vitaly Gerasimov ya mutu a birnin Kharkiv tare da wasu jami’an sojojin Rasha.
Hanyoyin sadarwa sun datse
Baya ga haka, jaridar ta ce kasar Ukraine ta fito da wata tattaunawa da aka yi tsakanin sojojin Rasha inda suke kokawa a game da halin da suke ciki a Ukraine.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An ji wadannan manyan sojoji su na magana a kan mace-macen da suka samu da kuma yadda duk na’urorin sadarwar da suke amfani da su, suka daina aiki.
Wani babban jami’in kasar Rasha, Christo Grozev ya tabbatar da mutuwar Janar Vitaly Gerasimov. Marigayin yana cikin kwararrun sojojin da ake takama da su.
Vitaly Gerasimov ya san yaki
Kamar yadda rahoton CNBC ya nuna, Janar Vitaly Gerasimov yana cikin sojojin Rasha da aka yi gumurzu da su a yakin Chechen na biyu da kuma na kasar Siriya.
An hallaka sojojin da suke karkashin Vitaly Gerasimov a yakin na Ukraine da Rasha ne a sakamakon matsalar hanyoyin sadarwa da aka samu a ‘fagen fama.
Janar 2 sun mutu a mako 1
Kafin wannan rashi da dakarun Rasha suka yi, an ji cewa mayakan Ukraine sun bindige Janar Andrei Sukhovetsky wanda yake jagorantar sojojin saman Rasha.
Hakan ya na nufin Vitaly Gerasimov shi ne Janar na biyu da Rasha ta rasa a Ukraine a mako guda.
Kasashen da ke da nukiliya
Ku na sane cewa kasar Rasha da Amurka ne a gaba a jerin kasashen da suka mallaki makaman nukiliya. Bayan su a wannan jerin sai irinsu Faransa da Birtaniya.
Kasar Rasha ta na da makamai fiye da 6200 na nukiliya; daga makamai masu linzami zuwa bama-bamai. Tun tale-tale, Rasha ta sha gaban kowace kasa a nan.
Asali: Legit.ng