Jerin kasashen Duniya 8 masu nukiliya da adadin makaman da suka mallaka a 2022

Jerin kasashen Duniya 8 masu nukiliya da adadin makaman da suka mallaka a 2022

  • Kasashe 8 sun sanar da Duniya cewa su na da makamin nukilya, kuma sun yi gwajin lafiyar makaman
  • Rasha, Amurka da Sin su na kan gaba a jerin wadannan kasashen, sai irinsu Faransa da Birtaniya
  • Kasar Israila ta mallaki nukiliya a boye, shekaru fiye da 50 kenan ta ki fitowa ta bayyana hakan

Rahoton da aka samu a shafin Wikipedia ya bayyana cewa kasashe takwas ake da labarin su na da makamai na kare dangi da aka fi sani da nukiliya.

Akwai kingiyar NPT ta wadannan kasashe wanda Koriya ta Arewa ta fita daga cikinsu a 2023. Ana tunanin kasar ba ta da wani makamin nukiliya mai aiki.

An yi kasashen da a baya sun mallaki nukiliya, amma yanzu ba su da komai. Akwai Afrika ta kudu, da kasashen URRS (Belarus, Kazakhstan, da Ukraine) a jerin.

Kara karanta wannan

Najeriya ta shiga cikin sahun kasashen duniya 141 da suka bukaci a hukunta Rasha

Yadda kason nukiliya yake

Jaridar ES ta kawo bayanin karfin wadannan kasashe da suke da makaman nukiliya a yau:

Rasha

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kasar Rasha ta na da makamai fiye da 6200 na nukiliya; daga makamai masu linzami zuwa bama-bamai. Tun tale-tale, Rasha ta sha gaban kowace kasa a nan.

Amurka

Akwai lokacin da Amurka ta mallaki makaman nukiliya 31, 000 a 1960. Ana kiyasin cewa a yau, ta na da manyan makaman nukiliya sama da 5500 masu lafiya.

Birtaniya da Faransa

Tsakanin 1952 zuwa 1960 aka samu nukiliya a Ingila da Faransa. Makaman Birtaniya sun ragu daga 500 zuwa 225, Faransa kuma ta na da makamai 300 har gobe.

Nukiliya
Makami mai linzami Hoto: www.afp.com
Asali: UGC

Sin

Sin ce karshen shiga jerin kasashe masu nukiliya. A 1964 kasar ta samu bam na nukiliya, yanzu maganar da ake yi, ta mallaki makamai masu linzami kusan 350.

Kara karanta wannan

Mun zo taya ku yakar Rasha: Dandazon 'yan Najeriya sun cika ofishin jakadancin Ukraine

Israila

Ana zargin kasar Israila da ta ke abin ta a asirce tana da makamai masu linzami tsakanin 75 zuwa 400. Tun 1967 kasar Israila ta fara wannan aiki ta bayan-fage.

Koriya ta Arewa

Kasar Koriya ta Arewa ta na da karfin da za ta iya mallakar nukiliya 40 zuwa 50. Zuwa yanzu ana tunanin abin da ta ke da shi bai wuce kananan makamai 10 ko 20 ba.

Indiya da Fakistan

Rahoton da ES ta fitar ya nuna a shekarar 1998 wadannan kasashe su ka samu karfin nukiliya. Indiya ta na da makamai kusan 150, yayin da Fakistan ta ke da 165.

Jerin kasa da kasa

Ga alkaluman nan filla-filla kamar yadda aka kawo a shafin World Population Review.

1. Rasha – 6255

2. Amurka – 5550

3. Sin – 350

4. Faransa – 290

5. Birtaniya – 225

6. Fakistan – 165

7. Indiya - 156

8. Israila - 90

9. Koriya ta Arewa – 0

Kara karanta wannan

Sabon jidali: Tallafin mai zai karu kan FG yayin da farashin mai ya tashi zuwa $112.7 kan kowacce ganga

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng