Russia vs Ukraine: Taliban Ta Faɗa Wa Rasha Ta Yi Sulhu da Ukraine

Russia vs Ukraine: Taliban Ta Faɗa Wa Rasha Ta Yi Sulhu da Ukraine

  • Gwamnatin Taliban na kasar Afghanistan ta yi kira ga kasashen Rasha da Ukraine su hau teburin sulhu domin warware rikicin da ke tsakaninsu
  • Daular musuluncin ta Afghanistan ta ce ta damu da yiwuwar asarar rayyuka da dukiyoyin farar hula da ka iya faruwa idan har kasashen biyu ba su ajiye makamai sun yi sulhu ba
  • Kazalika, Daular musulunci ta yi kira ga bangarorin biyu su mayar da hankali wurin tsare rayukan daliban Afghanistan da wadanda suka yi hijira zuwa Ukraine

Taliban ta yi kira ga Rasha da Ukraine sun warware rikicin da ke tsakaninsu ta hanyar lumana watanni bayan ta halaka mutanen da ba su ji ba ba su gani ba bayan karbar mulki a Afghanistan.

A cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin Twitter na Taliban, mai suna Islamic Emirate of Afghanistan, kungiyar mayakan ta ce tana damuwa bisa yiwuwar asarar rayukan farar hula.

Kara karanta wannan

Rasha vs Ukraine: Ku Rufa Mana Asiri, Ku Ja Bakinku Ku Yi Shiru, 'Yan Najeriya Sun Shawarci FG

Russia vs Ukraine: Taliban ta fada wa Rasha ta yi sulhu da Ukraine
Taliban ta fada wa Rasha ta yi sulhu da Ukraine. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

A karkashin wani hatimin hukumar harkokin kasashen waje na kasar - wanda ya yi kama da irin wanda Amurka ke amfani da shi - Taliban ta yi kira da cewa a yi zaman tattaunawa tsakanin Rasha da Ukraine kuma a tsare lafiyar yan Afghanistan da ke Ukraine.

A cikins sanarwar da aka wallafa a shafin Twitter na Taliban, kungiyar ta mayaka ta ce ta damu da yiwuwar asarar rayukan fararen hula a Ukraine.

Kawo yanzu, babu wata kasa da ta amince da gwamnatin na Taliban a Afghanistan tun bayan karbe mulki da ta yi da karfin soji a watan Agusta, rahoton Daily Trust.

Sanarwar ta ce:

"Daular Musulunci ta Afghanistan na saka ido kan halin da ake ciki a Ukraine kuma ta damu game da yiwuwar rasa rayyukan fararen hula."

Kara karanta wannan

Yakin Rasha da Ukraine: 'Yan majalisun Najeriya za su kwasho daliban Najeriya a Ukraine

Daular ta musulunci ta yi kira ga bangarorin biyu su kame kansu. Ya kamata dukkan bangarorin biyu su guji aikata abin da zai hassala rikicin.

A cewar wasu hasashe, fiye da fararen hula 1000 ne aka kashe, sannan 2000 suka jikkata sakamakon hare-haren da Taliban ta kai domin karbe Afghanistan.

An kuma kashe dakarun Afghanistan 1500, yayin da tsohuwar gwamnatin Afghanistan ta yi ikirarin cewa ta kashe yan taliban kimanin 10,000.

Sanarwar ta cigaba da cewa:

"Daular musulunci ta Afghanistan, bisa tsarinta na rashin bangaranci, tana kira ga dukkan bangarorin biyu su warware rikicin ta hanyar tattaunawa da lumana.
"Daular musuluncin kuma tana kira ga bangarorin biyu su mayar da hankali wurin tsare rayukan daliban Afghanistan da wadanda suka yi hijira zuwa Ukraine."

A cewar CNN, yan Afghanistan 370 ne suka bar kasarsu suka koma Ukraine a shekarar 2021.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164