Da Dumi-Dumi: Dakarun Rasha sun balla babban birnin kasar Ukraine

Da Dumi-Dumi: Dakarun Rasha sun balla babban birnin kasar Ukraine

  • Sojojin kasar Rasha tare da motocin yakin su sun fara kutsawa babban birnin ƙasar Ukraine ta hanyar yankin arewaci
  • Rahoto ya nuna cewa tun da safiyar Alhamis aka ji kara na tashi daga arewacin birnin Kyiv, kwana biyu da fara yaƙi
  • Shugaban kasar Ukraine ya yi kira ga shugaban Rasha Putin ya dakatar da wannan yakin ya duba yuwuwar tsagaita wuta

Dakarun kasar Rasha sun kutsa kai cikin Kyiv, babban birnin kasar Ukraine, a rana ta biyu da fara kaddamar da hare-haren soji cikin kasar.

A rahoton da BBC ta tattara, Hukumomi a kasar Ukraine sun tabbatar da cewa sojojin Rasha sun kutsa arewacin Birnin Kyiv.

A halin yanzun Motocin yaƙin sojojin Rasha sun shiga cikin babban birnin ta hanyar arewacin Kyiv, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Wani bawan Allah ya halaka babban abokinsa kan Lemun kwalba na N150

Motocin yaki
Da Dumi-Dumi: Dakarun Rasha sun balla babban birnin kasar Ukraine Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Shugaban ƙasar Ukraine Zelensky ya yi jawabi ga mutanen kasar tun ɗazun kuma ya yi kira ga shugaban Rasha Putin ya dakatar da wannan yaƙin ya duba yuwuwar tsagaita wuta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane hali mutanen birnin ke ciki?

Dubbannin mutane mazauna birnin Kyiv, a halin yanzun sun fara neman mafaka a tashohin jirgin ƙasa domin kaucewa yaƙin da ka iya faruwa bayan shigowar sojojin Rasha.

Wani Akawunta, Udovichenko, ya shaida wa kafar watsa labarai ta Aljazeera cewa ya ɗauki mahaifiyarsa yar shekara 82, Olha Krisevich, sun nufi wurin mafaka.

A ranar Alhamis, Ministan harkokin cikin gida na ƙasar Ukraine, ya sanar da cewa gwamnati zata hana yan ƙasa dake tsakanin shekara 18-60 yin gudun hijira.

Ya ce:

"Jami'an tsaron bakin Boda sun bada rahoton cewa bisa dokokin ƙasa, an hana wasu mazauna ƙasar fita na ɗan wani lokaci."

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya zata kwaso yan Najeriya dake zaune a kasar Ukraniya

"A takaice duk wani mazuanin Ukraine namiji dake tsakanin shekara 18 zuwa 60 an haramta masa ficewa daga ƙasa."

A wani labarin kuma Muhimman abubuwa hudu da ya kamata ku sani game da mataimakin gwamna Mahdi Aliyu da Majalisa ta tsige a Zamfara.

A ranar Laraba, 23 ga watan Fabrairu, 2022, majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige mataimakin gwamna, Barista Mahdi Aliyu Gusau.

Tun bayan sauya shekar gwamna Matawalle daga PDP zuwa APC, alaƙa tai tsami tsakanin su, mun tattaro muku abu hudu game da Gusau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262