Tana wasa da lafiyarta: Bidiyon yadda wata mata mai ciki ta zaƙe wurin kwasar rawa da ƙarfinta na bara

Tana wasa da lafiyarta: Bidiyon yadda wata mata mai ciki ta zaƙe wurin kwasar rawa da ƙarfinta na bara

  • Bidiyon wata mata mai juna biyu tana kwasar rawa a wani biki ya janyo cece-kuce a yanar gizo inda mutane su ka dinga tofa albarkacin bakunansu
  • Ba kamar yadda masu ciki su ke kasancewa ba, matar ta kwashi rawa da dukkan wani karfi da ke jikinta wanda mutane su ka dinga ihu su na kara mata kaimi
  • Yayin da wasu su ke yaba mata a kan jarumtar da ta nuna, wasu sun dinga caccakarta bisa sa rayuwarta cikin hatsari da kuma ta jaririnta

Wata mata mai juna biyu ta nuna karfi, bajimta da jarumta wanda ya janyo kowa ya watse aka bata fili a wani biki da ta je tana kwasar rawa.

Tana wasa da lafiyarta: Bidiyon yadda wata mata mai ciki ta zake wurin kwasar rawa da karfinta na bara
Bidiyon yadda wata mata mai ciki ta zake wurin kwasar rawa da karfinta na bara, mutane sun tofa albarkacin bakinsu. Hoto: @ssussjamofficial
Asali: Instagram

Sai dai kasancewarta mai ciki ya na nuna rashin kularta da rashin sanin ciwon kanta a kan yadda ta dinga rawar har wani zai musanta idan cikin gaske ne a jikinta.

Kara karanta wannan

Duk da yawaitar kashe-kashe, Shugaban ma'aikatan tsaro ya yi iƙirarin kalubalen ya ragu

Ta yi wani taku mai ban mamaki

A cikin gajeren bidiyo wanda @ssussjamofficial ta wallafa a shafinta na Instagram, an ga yadda mai cikin ta fara rawa tana kada kwankwasonta wanda ya dace kwarai da sautin da ke tashi a wurin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta sanya wani takalmi mai rufaffen sama da wasu matsattsun sutturu wadanda su ka nuna surarta kwarai hakan ya tabbatar da ta na da cikin.

Yayin da ta ke barar da rawan, mutane sun dinga ihu suna yaba irin jarumta da kwarewar da ta nuna a wurin bikin.

Ana zargin hakan ya faru ne a wani biki a Casablanca, kasar Morocco.

Ga bidiyon a kasa:

Tsokacin jama’a a karkashin bidiyon

@tammy_soloved ta ce:

“Nan da nan za ta haihu, sai dai matsala daya, ta na kammala rawar jaririn zai fara yi mata motsi ko ta ina.”

Kara karanta wannan

Rikici: Mata ta kai karar TikTok saboda samun matsalar kwakwalwa tsabar kallo a kafar TikTok

@nellie_di_don ta ce:

“Gaskiya mijin ta ne ya bar ta ta ke kwasar rawa ta na tozarta jaririn da ba ta haifa ba.”

@lexusunruly ya yi tsokaci da cewa:

“Anya, gaskiya wannan ba ciki ba ne, ciwo ne. Idan har ciki ne ba ta isa ta dinga wannan juyin ba."

@choymegan ya ce:

“Ni ban ga wani abu mara kyau da ta yi ba. Shi yasa wasun ku son jiki da rashin wayau ya ke sa ku tashi, ku ci abinci sai ku dangare a gado ku na bacci idan ku na da ciki.”

Shugaban wurin aiki ya ba na ƙasa da shi da ke tattaki zuwa wurin aiki kyautar mota

A wani labarin, kun ji wani matashi, Walter, ya yi tattakain mil 20 a ranar sa ta farko ta zuwa wurin aiki. Motar sa ta samu matsala ana gobe zai fara zuwa aikin hakan ya sa ya yanke wannan shawarar.

Kara karanta wannan

Angon Instagram: Yadda budurwa ta cire kunya tayi abin da ya dace, ta yi wuf da matashi

Kafin safiyar, ya yi kokarin tuntubar abokan sa amma babu alamar zai samu tallafi saboda ya sanar da su a kurarren lokaci kamar yadda Understanding Compassion ta ruwaito.

Daga nan ne ya yanke shawarar fara tattaki tun karfe 12am don isa wurin aikin da wuri. Matashin bai bari rashin abin hawan ya dakatar da shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164