An fitar da gwarazan gwamnonin bankunan Afrika, babu Emefiele na Najeriya a 10 na farko
- Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya zo na 15 a cikin takwarorinsa 26 a Afrika
- Global Finance ta ce Abdellatif Jouahria ya yi zarra a cikin gwamnonin manyan bankunan Afrika
- Tarek Amer da Abdellatif Jouahri su ne gaba a sahun gwamnonin bankunan kasashe na Duniya
Wani bincike da aka fitar a kan gwamnonin manyan bankunan kasashe na Duniya, ya nuna Mr. Godwin Emefiele shi ne na 15 a cikin gwamnoni 25 a Afrika.
Tun shekarar 1994 Global Finance ta saba fitar da alkaluma a kan gwamnonin bankunan manyan kasashe 101; daga ciki har da na Turai, Amurka da na Afrika.
Legit.ng ta samu rahoto cewa a shekarar 2020, Godwin Emefiele ne ya zo na 10 a nahiyar Afrika. Wannan karo ya sauka kasa a jerin, inda aka same shi a na 15.
Emefiele ya na bayan gwamnonin bankunan kasashe irinsu Masar, Moroko, Afrika ta Kudu da sauran makwabtansa kamar Botswana, Riwanda, da Uganda.
Sauran gwamnonin bankunan kasashen Afrika da duk sun fi Emefiele tabuka wani abu su ne: Angola, Ghana, Mauritius, Kenya, Tanzania, da kasar Aljeriya.
Ba a labarin Emefiele
Gwamnan babban bankin Moroko, Abdellatif Jouahri, da gwamnan bankin Masar, Tarek Amer, sun samu shiga sahun gwamnonin da suka yi kokari a Duniya a 2021.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gwamnonin bankunan Brazil, Bulgariya, Kanada, Chile, Sin, da Czech su na cikin mafi kokari.
Yadda ake tattara alkaluma
Global Finance ta na amfani da wasu ma’unan tattali irinsu yakar tsadar farashi, cigaban tattalin arziki, darajar kudin gida, da bashi da ruwa wajen fitar da alkaluma.
Ana ba kowane gwamnan babban banki maki daga A zuwa F. ‘A’ ya nuna cewa an yi kokari, yayin da gwamnan banki zai samu ‘F’ idan har ya gaza a wani bangaren.
Wani maki Godwin Emefiele ya samu
A karshe sakamakon Najeriya ya nuna gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya tashi ne da maki C. Hakan yana nufin babu yabo babu fallasa a kokarin da ya yi a 2021.
Gwamnan babban bankin na Najeriya ya gaza rike darajar Naira. Baya ga haka ana fama da tsadar farashin kaya. CBN kuma ya bar farashin bashi da ruwa ne kan 12.5%.
Za a ga amfanin Buhari wata rana
Mai ba shugaba Muhammadu Buhari shawara, Bashir Ahmaad ya ce sai can bayan kammala wa’adinsa sannan za a ci moriyar gyaran da Buhari ya yi a Najeriya.
Bashir Ahmaad, ya ce ’yan Najeriya ba za su ga amfanin mulkin Muhammadu Buhari a yanzu ba.
Asali: Legit.ng