Shugaban Afrika Ta Kudu ya kamu da Korona, Alamun ciwon sun fara bayyana a jikinsa

Shugaban Afrika Ta Kudu ya kamu da Korona, Alamun ciwon sun fara bayyana a jikinsa

  • Shugaban Kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya kamu da kwayar cutar korona amma alamun ba masu tsanani bane
  • Sanarwar ta ofishin shugaban kasar ta fitar ta ce likitocin Rundunar Sojojin Kasar Afirka ta Kudu suna kulawa da Ramaphosa
  • Ofishin shugaban kasar ta umurci dukkan wadanda suka san sun yi cudanya da Ramaphosa a baya-bayan nan su tafi su yi gwaji

Afirka Ta Kudu - Ana yi wa Shugaban kasar Afirka Cyril Ramaphosa magani bisa alamun cutar korona bayan gwajin da aka masa ya nuna ya kamu da cutar a ranar Lahadi, rahoton Arise News.

Sanarwar da ofishin shugaban kasar ta fitar ya ce baya jin dadi sakamakon kamuwa da cutar korona da ya yi.

Kara karanta wannan

Yari Vs Matawalle: Kotu ta yanke hukunci kan rikicin jam'iyyar APC a Zamfara

Shugaban Afrika Ta Kudu ya kamu da Korona, Alamun ciwon sun fara bayyana a jikinsa
Shugaba Ramaphosa na Afirka ta Kudu ya kamu da korona. Hoto: Arise News
Asali: Facebook

Ya kebe kansa a Cape Town kuma likitocin Rundunarr Sojojin Afirka Ta Kudu suna kulawa da shi a cewar sanarwar. Ya wakilta mataimakinsa David Mabuza ya cigaba da gudanar da harkokin mulki a mako mai zuwa.

Ramaphosa, mai shekaru 69, ya yi rigakafin korona. Sanarwar ba ta fayyace ko nau'in omicron na korona bace ya kamu da ita, Arise News ta ruwaito.

Ramaphosa ya ziyarci kasashen Afirka ta Yamma hudu

A makon da ta gabata, Ramaphosa ya ziyarci kasashen Afirka ta Yamma hudu. An yi wa shugaban kasar da iyalansa gwajin korona a duk kasar da suka tafi.

Ramaphosa ya ce kamuwar da ya yi da cutar zai zama darasi ga 'yan kasarsa su rika kiyaye wa sannan su yi riga kafi, a cewar sanarwar. Rigakafi ne hanya mafi inganci na kare kai daga cutar da kuma illolinta in ji sanarwar.

Kara karanta wannan

Ba zata saɓu ba, Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kisan Kwamishina a jihar Katsina

An shawarci wadanda suka yi cudanya da Ramaphosa su gwada kansu

Hakazalika, sanarwar ta bukaci dukkan mutanen da suka yi cudanya da Ramaphosa a ranar Lahadi su kula da kansu sannan su tafi su yi gwajin korona.

Jami'an lafiya sun ce kasar Afirka ta Kudu tana fama da sabuwar nau'in korona ta Omicron.

An samu kimanin mutum 18,000 da suka kamu da korona zuwa daren ranar Lahadi. Fiye da kashi 70 cikin 100 cikinsu sun kamu ne da sabon nau'in na Omicron a cewar bincike.

Binciken masana ya nuna cewa nau'in na Omicron ya fi sauran na baya saurin yaduwa amma alamunsa ba su kai sauran hadari ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164