Rashin tsaro: Shugaban Rasha, Putin ya yi wa Gwamnatin Buhari muhimmin alkawari
- Vladimir Putin ya ba Najeriya tabbacin gwamnatin kasar Rasha za ta ba ta gudumuwa
- Shugaban na Rasha yace za su taimakawa gwamnatin Najeriya wajen yaki da ‘yan ta’adda
- Putin ya bayyana haka ne da Jakadan Najeriya, Farfesa Abdullahi Shehu ya kai masa ziyara
Russia - Yayin da ake kokarin kawo karshen Boko Haram da sauran ‘yan ta’adda a Najeriya, shugaba Vladimir Putin ya yi alkawarin taimakawa Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin yace zai yi bakin kokarinsa wajen maganin duk wasu ‘yan ta’adda a kasar nan.
Vladimir Putin ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin Jakadan Najeriya zuwa Rasha, Farfesa Abdullahi Shehu wanda ya gabatar da takarda gare shi.
Da yake bayani a fadar gwamnati ta Kremlin, Putin yace gwamnatinsa za ta yi duk abin da za ta iya domin kauda masu tsattsauran ra’ayin addini a duk Duniya.
Alakar Najeriya da Rasha
Putin ya yi magana kan dangantakar da ke tsakanin Najeriya da kasar Rasha, yace za su tattauna a kan yadda za a magance ta’addanci da sauran wasu matsaloli.
The Guardian ta kawo rahoto a ranar 2 ga watan Disamba, 2021, inda aka ji Putin ya na cewa Rasha a shirya take ta amfana da kasashe, kuma a amfana da ita
Shugaban yace za a cin ma wannan idan akwai ganin girma da mutunta juna, tare da jan-kunne ga kasashe su guji yi wa junansu katsalandan cikin harkokinsu.
Kawo karshen COVID-19
Har ila yau, an rahoto Putin yana fadawa Farfesa Shehu cewa Rasha ta kirkiro maganin cutar COVID-19, kuma ta shirya raba shi ga sauran kasashen Duniya.
Ganin yadda cutar COVID-19 ta addabi kasashe a yau, Putin yace sun kirkiro maganin wannan cuta, kuma duk kasar da take da sha’awa, sai tayi mata magana.
Jakadan Najeriya a Rasha ya ji dadin wannan tattaunawa da ya yi da Vladimir Putin, har ya kara masa da cewa takwaransa, Muhammadu Buhari ya na gaida shi.
Kul aka raba Najeriya - Osinbajo
Yemi Osinbajo ya ce Muhammadu Buhari na bakin kokarinsa, ya kuma yi alkawari: Gwamnatin APC za ta kawo karshen matsalar rashin tsaro kwanan nan.
Farfesa Yemi Osinbajo ya kuma ja-kunnen mutane da cewa neman a raba kasar nan ba zai haifar da ‘da mai ido ba, sai karin wahala da za ta nunku a Najeriya.
Asali: Legit.ng