An gano abin da Buhari ya fadawa Shugaban kasar Afrika ta Kudu kafin ya lula zuwa Dubai
- A jiya ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da Cyril Ramaphosa a fadar Aso Rock.
- Muhammadu Buhari ya bayyana muhimmancin hadin-kai tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu
- Bayan wannan tattaunawa ne sai shugaban kasar ya kama hanya zuwa garin Dubai a kasar UAE
Abuja - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yace Najeriya da kasar Afrika ta Kudu na bukatar su karfafa alakar mutum-da-mutum da ke tsakaninsu.
Jaridar The Cable ta rahoto shugaban kasar ya na mai cewa akwai bukatar ayi hakan domin a magance mummunar takara tsakanin ‘yan kasashen biyu.
Buhari ya yi wannan bayani ne a ranar Laraba, 1 ga watan Disamba, 2021 a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban kasar Afrika ta kudu, Cyril Ramaphosa.
Da duminsa: Yayinda ake gudun Omicron, Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Shugaban kasar Afrika ta Kudu
Shugaba Ramaphosa ya ziyarci garin Abuja ne domin halartar taron BNC na kasar Najeriya da Afrika ta Kudu wanda wannan ne karo na goma da aka yi.
A jawabinsa, Buhari ya ce da gaske yake yi wajen gyara dangantakar da ya kira ta musamman da kasar Afrika ta Kudu wanda ya ce hakan zai taimaki Afrika.
An rahoto shugaban Najeriyar ya na cewa kyakkyawar alakar kasarsa da takwarar ta su za ta bunkasa sha’anin ilmi, kimiyya, kasuwanci, bude ido da tsaro.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jawabin Muhammadu Buhari
"Ka ba ni dama in bayyana wasu kalubule da muka gano a wajen taronmu na BNC na karshe, wadanda har yau ba a shawo kansu ba.”
“Dole mu tabbatar da an gyara alakar mu da mutum-da-mutum har ya zama babu bukatar mu rika takara ta kishiyantar junanmu.” - Buhari
“A wannan bangare, dole mu karfafa sha’anin ilmi da kimiyya, sufuri, bude ido, shirye-shirye na matasa, kasuwanci da karfin soja da sauransu.”
“A wannan gaba, bari in jaddada yunkurinmu na samum dangantaka mai kyau tsakanin kasashenmu biyu. - inji Shugaban kasar Najeriya
Da yake magana a Aso Villa kafin ya bar Najeriya, Buhari ya yabawa kasar kudancin Afrikar a kan shigo da wani tsari da tayi domin hada kan matasan kasashen.
Man fetur zai kara kudi a 2022
A farkon makon nan ku ka ji cewa tsadar da man fetur zai yi a gidajen mai a shekara mai zuwa ya zarce yadda hukumar mai na kasa watau NNPC ta ke tunani.
'Yan kasuwa sun ce ‘yan Najeriya za su ga karin kusan 110% a farashin litar fetur a shekarar 2022.
Asali: Legit.ng