Turawa sun fara dawo da zanen da suka sace a Najeriya shekaru 120 da suka wuce

Turawa sun fara dawo da zanen da suka sace a Najeriya shekaru 120 da suka wuce

  • Wata kwaleji dake karkashin jami’ar nan ta Cambridge za ta dawo da kayan da aka sace a Najeriya
  • A shekarar 1897 dakarun sojojin Birtaniya suka yi gaba da wasu gumaka daga masarutar Benin
  • Wadannan kayan tarihi sun yi shekara da shekaru a kasar Ingila, yanzu za a dawo da wasunsu

England - Kwalejin Jesus College, wanda tana cikin jami’ar Cambridge za ta dawo da wasu zanen gumaka da sojojin Birtaniya suka dauke daga Najeriya.

Punch ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 27 ga watan Oktoba, 2021 cewa jami’ar da ke Birtaniyar za ta maidowa masarautar kasar Benin wadannan kayan.

Tun a shekarar 1897 ne wasu dakarun Turawan mulkin mallaka suka yi awon gaba da wadannan kayan kyele-kyele, shekaru kimanin 124 da suka wuce.

An yi alkawari za a dawo da wadannan kaya ne a ranar Alhamis din ta gabata. Ana sa rai hakan zai taimaka wajen dawo da ragowar kayan da aka dauke.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun tafi kotu, sun bukaci a raba Najeriya, a ware 'yan wani yankin kudu

Wannan karo an cin ma yarjejeniya za a dawowa masarautar Benin wani zakara da aka sassaka da tagulla shekaru sama da 120 da suka wuce a kasar Benin.

Zanen Benin
Gunkin zakaran da aka dauke a 1897 Hoto; www.reuters.com
Asali: UGC

Kayan ado da tarihi

Wadannan zane sun kasance tarihi a Najeriya da kasashen Afrika, amma Turawan na Ingila suka sace su, suka adana a gidajen tarihin su a kasar Birtaniya.

Wata jami’ar wannan kwaleji, Sonita Alleyne ta bada tabbacin kayan za su dawo inda aka dauke. Alleyne ta fitar da jawabi kafin bikin maido da gumakan.

“Abin da ya kamata kenan, saboda sanin darajar tarihi da gadon da suka yi.” - Sonita Alleyne.

Gwamnatin Najeriya ta yi magana

Reuters tace Ministan labarai, Lai Mohammed ya godewa kwalejin a kan wannan, yace suna fata a dawo da duka kayan tarihin Najeriya da ke kasashen waje.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

Wannan ne karon farko da kayan da aka dauke za su dawo Najeriya. Ana sa rai a shekara mai zuwa, Kasar Jamus ta dawo da irin wannan kaya da ta dauka.

Dr. Uchechi Iweala ya ciri tuta

A makon nan ne yaron Ngozi Okonjo-Iweala watau Dakta Uchechi Iweala ya yi wa wani Bawan Allah aiki a gadon bayansa a wani asibiti da ke garin Maryaland.

Uchechi Iweala kwararren Likita da ake ji da shi a kasar Amurka. Likitan ya yi karatu a Harvard da wasu Jami’o’i dake New York da babban birnin Washington DC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng