Barewa ba ta gudu: Yaron da Ngozi Okonjo-Iweala ta haifa, ya kafa tarihi a Duniyar kiwon lafiya
- Dr. Uchechi Iweala ya shiga cikin littafan tarihi bayan wani aiki da ya yi a cikin kashin gadon-baya
- Uchechi Iweala yana cikin likitocin farko da suka fara yin irin wannan aiki a asibitocin Maryland
- Tsohuwar Ministar kudin Najeriya, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ce ta hafi wannan kwararren likitan
United States - Dr. Uchechi Iweala wanda ‘da ne a wurin Dr. Ngozi Okonji-Iweala ya kafa sabon tarihi a birnin Maryland da ke kasar Amurka.
BBC tace Ngozi Okonjo-Iweala ta taya yaron na ta murnar zama daya daga cikin likitocin farko a Maryland da ya yi wa mutum aiki a gadon baya.
Tsohuwar Ministar Najeriyar wanda yanzu ta ke shugabantar kungiyar kasuwanci na Duniya, WTO, ta fito tana alfahari da Dr. Uchechi Iweala.
A ranar Alhamis, 28 ga watan Oktoba, 2021 ta tabbatar da wannan rahoto, tace yaronta ya fede wani Bawan Allah, ya yi masa ciko a kashin baya.
Maganar Ngozi Okonjo-Iweala
“Ina taya murna ga Dr. Uchechi Iweala, wanda ya zama daya daga cikin likitocin farko a Maryland da suka yi fida, suka gyara kashin gadon-baya ta hanyar amfani da mutum-na'ura.”
“Ina alfaharin zama mahaifiyarka! A cigaba da bada himma!” - Ngozi Okonjo-Iweala.
Jaridar Punch tace tsohuwar Ministar tattalin arzikin na Najeriya ta wallafa hotunan Uchechi Iweala a asibiti a lokacin da yake tsakar wannan fida.
Wanene Dakta Uchechi Iweala?
Rahoton ya bayyana cewa Dr. Iweala kwararren likita ne wanda ya yi suna wajen gyara kashin baya a cibiyar aiki ta kashi da ke Maryland, kasar Amurka.
Dr. Iweala ya yi digirinsa na farko da na biyu a ilmin likitanci a jami’ar nan ta Harvard, sannan ya kammala karatun kwarewa a jami’ar George Washington.
Dr. Iweala ya kware a aiki a gadon-baya a jami’ar birnin New York. Likitan yana iya yin ciko a kashin baya, ko ya yi aiki cikin lakar ba tare da an ji zafi ba.
Za a damkawa Amurka Abba Kyari?
Sufetan ‘Yan Sanda na kasa, Usman Alkali Baba, yace ba shi da labarin Amurka ta bukaci a damka mata Abba Kyari kamar yadda ake ta yada jita-jita.
IGP yace shi ma a kafafen sadarwa ya ji wannan labari, yace babu irin wannan rokon a gabansa.
Asali: Legit.ng