Abdullahi Abubakar
3562 articles published since 28 Afi 2023
3562 articles published since 28 Afi 2023
Jam'iyyar PDP a jihar Ekiti ta gabatar da rahoto ga kwamitin ladabtarwa bayan binciken tsohon gwamnan jihar, Ayodele Fayose inda ya bukaci a kore shi daga jam'iyyar.
Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya caccaki shugabanni kan rashin aiwatar da tsare-tsaren da suka kawo inda ya ce kwata-kwata ba su aiwatarwa.
Rikicin cikin gida na jam'iyyar APC a jihar Sokoto ya sake dagulewa kan wanda zai jagorance ta tsakanin Sanata Aliyu Wamakko da Sanata Ibrahim Lamido.
Babbar Kotun Tarayya ta tura gargadi ga shugaban hukumar DSS kan kin ba lauyoyin Nnamdi Kanu damar ganawa da shi duk mako da cewa za a tura shi gidan yari.
Ana ta yada labarin cewa hafsan sojojin Najeriya, Laftanar janar Taoreed Lagbaja yana fama da matsanancin rashin lafiya wanda har an fara neman kujerarsa.
Hukumar zaben jihar Kogi (KSIEC) ta sanar da zaben kananan hukumomi 21 da aka gudanar a jiya Asabar 19 ga watan Oktoban 2024 inda ya ce APC ce ta yi nasara.
Shugaban gwamnonin Arewa, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya jajantawa al'ummar jihar Jigawa kan iftila'i da ya afku inda suka ba da gudunmawar N900m.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon shugaban Najeriya, Janar Yakubu Gowon murnar cika shekaru 90 inda ya ce yana ba shi shawarwari masu kyau.
Wasu yan bindiga sun tarwatsa taron jam'iyyar LP a jihar Abia inda suka yi garkuwa da jiga-jiganta ciki har da mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa.
Abdullahi Abubakar
Samu kari