Kungiyar Izalah ta halarci taron majalisar shugabannin addinin Musulunci ta Duniya
Shugabannin kungiyar addini ta Jama'atu Izalatul bidi'a wa iqamatus Sunnah (JIBWIS) wacce akafi sani da kungiyar Izalah sun samu daman halartan taron majalisar Musulunci ta duniya da aka saba gudanarwa a kasar Saudiyya.
Kungiyar ta halarci wannan taro ne sakamakon goron gayyatar da ta samu daga hannun gwamnatin kasar Saudiyya.
Shugaban kungiyar, Sheik Abdullahi Bala Lau, tare da wasu manyan malaman kungiyar ne suka halarci wannan taro wanda ya hada da babban malamin addini na jihar Katsina, Sheikh Yakubu Hassan Sautus Sunnah.
KU KARANTA: Ya zama dole Buhari ya janye tallafin man fetur –Kwararre akan tattalin arziki
Legit.ng ta samu wannan rahoto daga shfin ra'ayi da sada zumuntar kungiyar inda suka saki jawabin cewa:
"Kungiyar IZALA ta halarci taron majalisar musulunci ta Duniya (Rabitah) ko a turance (Muslim World League) wanda ke gudana a halin yanzu a birnin Makkah dake kasar saudi Arabia.
Sheikh Imam Dr. Abdullahi Bala ya samu gayyata daga kasar saudiyya a madadin kungiyar Izala, inda ya samu rakiyar Sheikh Yakubu Musa Hassan, Dr. Ibrahim Abdullahi Rijiyan Lemu da Maitaimakawa shugaban akan Dukkan Harkoki (S.A. General Duties) Alh. Musa Hassan Isah."
Wannan taro ne dake game dukkan shugabannin addinin Musulunci a duniya inda ake tattauna wasu mas'alolin da suka shafin rayuwar Musulmai da addini a fadin duniya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng