Buhari da Sultan na cikin musulmai mafi shahara a Duniya
Yan Najeriya 13 ne aka shigar da sunayensu cikin jerin mutane 50 da suka fi shahara a duniyar musulunci, ciki har da shugaban kasa Muhammadu Buhari, mai alfarma Sarkin Musulmi, da Sheikh Ibrahim Saleh na jihar Barno.
Shugaba Buhari ne na 17 a jerin, hakan na nuna ya kara yin sama kenan daga matsayin na 20 da yake a bara, inda mai alfarma Sarkin Musulmi yake matsayi na 22, daga na 24 da yake a bara. Anyi ma jerin sunayen taken ‘musulmai 500 a duniya da suka fi shahara’ kuma an fitar da shi ne a ranar alhamis, 6 ga watan Oktoba, inda ya nuna yawan musulmai a duniya ya kai biliyan daya da miliyan dari bakwai (1.7 billion).
Dauke a cikin jerin sunayen har da na shugaban kungiyar musulmi ta Ansar-Ud-Deen na Najeriya Dakta Abdulrahman Olanrewaju Ahmad, Dr Ibrahim Datti Ahmed, Prince Bola Ajibola, Imam Muhammad Ashafa, Sheikh Tahir Usman Bauchi, Alhaji Aliko Dangote, Sheikh Yakubu Musa Katsina, Prof Ishaq Olanrewaju Oloyede, Emir of Kano Sanusi Lamido Sanusi II, shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau da shugaban addinin shi’a Sheikh Ibraheem Zakzaky, sai dai basa cikin jerin mutane 50 na farko.
KK KARANTA: "Masu kunan bakin wake, Yan Wuta ne"- Sarkin Musulmi
Rahoton yace mutane 500 da aka lissafa sun jagoranci akalar al’ummar musulmi, ta hanya mai kyau ko mara kyau, ya danganta da fahimtar mutane. “idan aka duba jerin mutane 50 na farko, za’a gane cewa dukkanin su kodai malamai ne ko shuwagabannin kasashe ne. ba za’a taba banzatar dasu ba, musamman ma shuwagabannin kasashe wanda suke nada malamai.”
Ga sunayen jerin mutane 50 na farko
Asali: Legit.ng