Mahauta da yan kungiyar asiri sun kara

Mahauta da yan kungiyar asiri sun kara

- Mahauta da yan kungiyar asiri sun kara a jihar Lagas, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane biyu

- An rahoto cewa Mahautan sun dauki fansar kashe daya daga cikinsu

- Yan kungiyar Asirin sun kashe wani mahauci Adewale Fakunle a hanyan Tolu dake jihar Lagas.

Mahauta da yan kungiyar asiri sun kara
Mahaucin da aka kashe, Adewale Fakunle

Mahautan da aka fi sani da ‘eleran’ wadanda suke kasuwar Alayibiaga a yankin Ajegunle dake jihar Lagas sun kara da wasu yan kungiyar asiri daga unguwa daya, wanda yayi sanadiya mutuwar daya daga cikin yan kungiyar asirin da kuma daya daga cikin mahautan.

KU KARANTA KUMA: Uba yayi ma yarsa ciki

An rahoto cewa rikicin ya fara ne a daren ranar Talata, 4 ga watan Oktoba, lokacin da yan kungiyar asirin suka kashe daya daga cikin mahautan suka kuma ci gaba a ranar Laraba, 5 ga watan Oktoba wanda ya kuma yin sanadiyar mutuwar wani daya, sata da kuma raunuka.

Wani mahauci wanda ya kasance direban motar kasuwa, ya hadu da wasu kungiyar yan asiri a hanyarsa ta dawowa daga gurin biki a ranar Talata da misalign karfe 10 na dare.

Kuma a lokacin yan kungiyar asirin sun gaman shan kashi kenan a hannun kungiyar adawa, wannan ne yasa suka wuce haushin su a kan mutumin, Adewale Fakunle, suka yi mai fashi, sannan kuma sukayi mashi dukan tsiya.

Sun kai ma direban motan kasuwa harin da har saida ya rasa inda kansa yake tare da adduna suka kuma barshi cikin jini ya mutu.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa bamu saki Sambo Dasuki ba

Duk da haka, yayi kokarin jan jiki zuwa gidan sa unguwar Baale Aiyetoro gida mai lamba 14, wanda daga nan ne aka yi gaggawan kai shi asibiti, inda aka tabbatar da mutuwan sa.

Duk da tabbaccin da jami’an tsaro suka ba mazauna gurin da yan kasuwa sunce har yanzu suna cikin tsoro kan yihuwar kuma ta da rikicin. Wasu daga cikin yan kasuwan sun ki bude shagunansu duk da cewan jami’an tsaro na nan.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel