Barayi sun yi wa Tauraruwa Kim Kardashian sata

Barayi sun yi wa Tauraruwa Kim Kardashian sata

- Wasu ‘yan fashi sun yi wa Tauraruwar nan ta duniya Kim Kardashian sata a Ranar Litinin

- Wannan abu ya faru ne da safiyar Shekaran jiya a dakin Otel din ta a Birnin Faris

- Tauraruwa Kim Kardashian tana auren mawakin nan Kanye West

Barayi sun yi wa Tauraruwa Kim Kardashian sata
Zoben Tauraruwa Kim Kardashian da aka sace

 

 

 

 

Wasu Barayi ‘yan fashi sun yi wa Tauraruwar nan ta duniya da aka sani Kim Kardashian gagarumar sata a Ranar Litinin da safe. Barayin sun kutsa dakin Otel din fitacciyar Tauraruwar ne Birnin Faris.

Barayin sun sace mata makudan kudi da dama, sun sace wani zoben da ke hannun tauraruwa Kim na fiye da dala miliyan 10, sannan kuma dauki wasu kayan da dama. Wadannan kudi wanda idan aka yi lissafi a kudin Naira na Najeriya sai su kai har Naira Biliyan uku.

KU KARANTA: Bakaken Aljanu sun kama wani Dan Majalisa

Da Naira biliyan uku kuwa a Najeriya sai ka saye Kungiyar kwallon kafar Rangers, wanda ta lashe Gasar Premier bana. Biliyan uku za ta saya maka irin gidajen da Linda Ikeji ta mallaka guda 6 a Legas. Naira Biliyan uku ta isa ka saye motar na ta Rolls Royce Phantom irin ta Ooni na Ife guda shida. Da Naira Biliyan uku sai ka saye filin wasan Najeriya da ke Surilere. Kai Naira biliyan uku dai ba kankanin kudi bane. Sai dai tauraruwar tace ita ta lafiyar ta take.

Kim Kardashian tana auren Babban mawakin nan Kanye West, suna da yaro mai suna North, watau North West. Tayi fice da sauran ‘yan gidan su a duniya, ana kiran su Kardashians.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng