Daliban Jami’ar ABU sun kera jirgi mai yawo da kan sa

Daliban Jami’ar ABU sun kera jirgi mai yawo da kan sa

- Wasu daliban Jami’ar ABU ta Zariya sun kera jirgin da ke yawo ba tare da direba ba

- Shettima A Kyari da abokan sa Aliyu Tanimu Muhammad, da kuma Abdurrazak Abdurraheem suka yi wannan gagarumin aiki

Wannan dai aikin kundin digirin su ne, ko dan nan gaba Shettima zai so ya fadada wannan aiki idan ya samu sukuni

Daliban Jami’ar ABU sun kera jirgi mai yawo da kan sa

 

 

 

 

 

Ga jirgi ya tashi shi kadai, kuma ya gama shawagin sa, ya sauka abin sa...

A wancan makon mun kawo maku rahoton yadda wani dalibin Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya mai suna Shettima Ali Kyari ya kera jirgin sama-mai yawo ba tara da matuki ba. Wannan karo Muhammad Malumfashi daga NAIJ Hausa ya samu damar zama da shi musamman domin jin ainihin yadda abin yake.

Ko da na samu ganawa da Shettima, sai ya mani bayani cewa wannan aikin jirgin, hadaka ne, shi da wasu abokan karatun sa; Aliyu Tanimu Muhammad da kuma Abdurrazak Abdurraheem. Wannan dalibai uku (wadanda ake kira da 3 Idiots a Makaranta) sun yi wannan aiki ne a matsayin kundin digirin su na farko a fannin Ilmin kimiyyar ’Physics’ a Jamiar Ahmadu Bello, Zaria.

KU KARANTA KUMA: Kasar tukunya ya zama magani?

Shettima ne wanda ya dauki nauyin aikin lantarki-wanda dama can yana da diploma a fannin wutan lantarki daga Makarantar Nuhu Bamalli, shi kuma Aliyu Tanimu Muhammad ya dauki nauyin aikin kere-kere da kuma kayan da ya kamata ayi amfani da su, Abdurrazak ya dauki nauyin tada jirgin sararin samaniya da kuma sauran bincike.

Daliban Jami’ar ABU sun kera jirgi mai yawo da kan sa

 

 

 

 

 

 

Aliyu Tanimu Muhammad Shettima Kyari Ali da kuma Abdurrazak Abdurraheem. Ana kiran su 3 Idiots a Makaranta

Shettima ba bako bane a harkar Jiragen sama, ko Firamaren sa dai a makarantar Aviation Staff School yayi, makarantar koyar da tukin Jirgin Sama a Najeriya, ya kuma yi kwas na watanni a Bangaren kula da Jirgin Saman a Makarantar koyon tukin jirgi ta Zariya-tare da daya daga cikin abokan aikin sa, Abdurrazak Abdurraheem.

Shettima ya dade yana burin kera jirgin sama, kamar wanda zai zama yana sintiri, yana yawo domin kula da Makarantar su ta ABU da ke Zariya, yace hakan zai yi maganin barayi. Mahaifin sa, wanda Injiniya ne a Makarantar koyon tukin jirgi, ya tabbatar masa da cewa hakan ba zai gagara ba. Watau a samu jirgi mara direba, mai kuma dauke da na’urar daukar hoto da kuma abin daukar Magana, kai har da ma na’urar da ke gane hayaki.

Abin kamar wasa, sai ga jirgi ya tashi wancan makon, an gwada sa lafiya lau a Filin wasanni na Jami’ar ta Ahmadu Bello ta Zariya. Wannan jirgi ya tashi a gaban Malamin da ke kula da wannan aiki Dr AA AbdelMalik da kuma Shugaban sasshen ‘Physics’ Dr. YI Zakari da ma wasu dabam da suka shaida. Anyi aikin kera wannan jirgi ne a dakin karatu na sashen Mechatronics da ke Jami’ar ta ABU Zariya, wani kwararre a wajen, Malam Aliyu ya taimaka sosai wajen ganin yiwuwar wannan aiki.

Abin ban sha’awa shine su Kyari sun hada wannan jirgi ne da kayan gida; irin su karfen labule, gwangwani, soso, langa-langa, kwali, katako dsr. Fiffiken jirgin na wani irin kwali ne maras nauyi, cikin sa kuma akwai wani dan guntun katako domin tsaida shi kikam a iska idan ya tashi. Kai, har tayan jirgin kuwa yana dauke ne da gwangwanin lemu na ‘Coke’ da kuma wani soso, saboda a samu dadin sauka a Kasa. Abin dai sai wanda ya gani. Wani Jami’in makarantar koyon tukin Jirgi da ke Zariya, wanda masani ne a harkar, Mista Chiwaitalu O. Tijjani ya taimaka wajen samar da wasu kayan da ake bukata, irin su Injin jirgin; wanda na DC Motor ne, abin da suke kira RC ko Radio Control.

KU KARANTA: Dalibin ABU ya kera jirgin sama mai yawo

Shettima asalin sa Babarbare ne daga jin sunan sa, Tanimu kuma dan kabilar Kakanda ne, shi kuma Abdulrrazak bayarabe ne, amma kusan duk suna zaune a Zariya. Watakila hakan ta sa Shettima ya sanyawa wannan jirgi suna HopeForChibokGirls, watau dai da rabon ganin yaran na Chibok da Yan Boko Haramnan suka sace.

A cewar Shettima, ya zama dole kowa yayi hobbasa a Kasar kamar dai yadda aka ce ChangeBeginsWithMe ma’ana canji ya fara daga kashin kai na. Shettima yace ya ga ya dace suyi abin da ya wuce zallan kira kamar BBOG, yace a matsayin su na daliban makaranta, suka ce bari su hada abin da zai taimakawa Najeriya.

Daliban Jami’ar ABU sun kera jirgi mai yawo da kan sa

 

 

 

 

 

 

HopeForChibokGirls

A wani lokaci da su Shettima suka je yawon bude ido daga makarantar su zuwa NIG com Sat, masu kula da na’urar tauraron dan adam na Najeriya da ke samaniya, sai ya fahimci ashe yana yiwuwa a kera irin wannan jirgi da zai taimaki bil adama, ba wai kawai aikin sa wutar yaki ba.

Ko don nan gaba, musamman shi Shettima Ali Kyari, yana da burin fadada wannan aiki.

Irin wannan jirgi zai iya jiwo kanshin hayaki daga nesa, ya kuma bada shela a dakin lura, ya kuma zama yana iya daukar hoto yayin da yake tafiya, hakan za ta sa a gane duk inda ya ke. Bugu da kari kuma ya zama yana dauke da na’urar jin sautin magana. Idan an samu yadda ake so, sai wannan jirgi ya je Kaduna ya dawo ba tare da wani ya tuka sa ba. Tirkashi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel