Yarinyar da ta haihu tun tana Firamari
- Wannan labari ne mai taba zuciya sosai amma duk da haka akwai darasi a ciki
- Uriemu Onome ta yi ciki a lokacin da take makarantar firamari tana da shekaru 11
- Iyayenta sun kore ta kana bun kunya da ta kawo wa gidansu. Ta koma kauye gurin kakarta wacce ba aiki takeyi ba
Ta gane kuskuren da tayi ta kuma dauki darasi don ta gyara. Yaya rayuwar abun kunyan da ta aikata ta kasance kuma me ya faru da danta. Onome ta bayyana labarinta mai ban al’ajabi a shafin Facebook. Karanta a kasa:
“Labari na ya faru shekaru 20 da suka wuce, nayi butulci da kuma miyagun abokai. Mahaifina ya kasance mutun mai tsauri; mahaifiyata a bangarenta mutun ce mai saukin kai da sanyi kuma tana barin mu munyi yadda muka ga dama. Tana mara mana baya musamman ni na kasance mace guda cikin yaya 3 da ta Haifa.
“Na yi tsauri har na fara yawo da miyagun abokai, nayi ciki a shekaru 11 (ina aji 5 a makarantar firamari) tun daga lokacin ne rayuwa ta sauya mun. tun daga lokacin ne rayuwa ta juya mun baya na kuma fita daga makaranta, har ya kai ban rubuta jarabawar zangon farko ba wato na firamari.
“Makwabtanmu suka fara mun izgilanci da habaici, mahaifina ya kasa jure hakan, don haka sai ya koreni daga gida don haka na koma zama tare da kakata. Domin na ciyar da kaina da bukatuna (kakata bata aiki) dole na garfafa wa kaina gwiwa don na yaki shaidan.
“Na san cewa ni na jawo ma kaina matsalar da ya same ni ban daura laifin a kan mahaifiyata ko wani ba. Na fara talla a titi inda nake siyar da garrin kwaki da ganda, pure water da sauransu.”
Yan watanni kadan na haifo Dana namiji da taimakon kudin da na hada (ta hanyar talla) Wanda nayi amfani da shi na rubuta jarabawar firamare, na kuma ci.
Duk da haka cikin sana'ar talla, na dauki nauyin kaina har na gama makarantar sakandare; na mayar da hankali domin na yi danasanin rayuwata na baya, na zama ya mai kwazo. Na rubuta jarabawar sakandare (waec) na kuma ci dukkan jarabawar da JAMB na kuma samu shiga makarantar jami'a."
Lokacin da mahaifina yaga na nutsu na kuma gane kurena, sai suka dawo dani da Dana gida, suka kuma turani jami'a suka rike mun Dana.
In takaita maku labarin, a yanzu haka na gama jami'ar jihad Lagas Akoka, na zama cikakkiyar malama kuma nayi aure cikin ikon Allah. Dana kuma yana mataki na 2 a jami'a yanzu inda yake karantar fannin shari'a. Ya zama kaman kani na a yanzu saboda tazarar mu ba mai yawa bace. Ya na da tsawo sosai.
Dana shine rayuwata, shine dalilin da ya sa na kai matakin da kai a rayuwa saboda zuwan shi duniya ne ya canza ni. Ya San abunda na fuskanta a rayuwa yana kuma kokarin ya gannin cikin farin cikin.
Asali: Legit.ng