Shugabar karamar hukumar Argungu tayi jawabi

Shugabar karamar hukumar Argungu tayi jawabi

– Budurwar nan da aka nada Shugabar Karamar Hukuma a Arewacin Najeriya tace ba ta da wani mugun nufi ga kowa

Hindatu Umar tace ba ta da wani dan adawa a Karamar Hukumar Argungu

– Mutanen Arugungun suna gani cewa ba ta dace ta Shugabancin Karama Hukuma ba

Shugabar karamar hukumar Argungu tayi jawabi

 

 

 

 

 

Buduwar nan da aka nada matsayin Shugaban Karamar Hukumar Arugungun dake Arewa maso Yammacin Jihar Kebbi tayi jawabi ga Gidan BBC, inda ta ce ita ba ta da wani wanda ta dauka dan adawa a Garin. Hindatu Umar tace duk da irin rashin goyon bayan da sukar ta da ake yi, ba ta rike kowa a zuci ba.

Hindatu tace ita fa aiki kawai ta sa gaba a Karamar Hukumar ta Arugungu, don haka ba ta rike kowa da mugun nufi a zuciyar ta ba. Hindatu tace yanzu lokaci ne na canji, Allah kuma ya kawo canji, ya kai har matasa ma irin ta ana damawa da su. Hindatu tace abin da mutanen Karamar Hukumar ya kamata suyi shine su godewa Allah.

KU KARANTA: An nada yarinya mai shekaru 25 a matsayin Shugabar Karamar hukumar Argungu

Hindatu ta shaidawa Gidan Rediyon BBC Hausa cewa, ba ta taba tunanin a rayuwa za ta zama Shugabar Karamar Hukuma ba, tace ita can da, burin ta ta zama Malaman makaranta. Sai dai Ubangiji ya nufi ta jagoranci Karamar Hukumar Arugungun. Hindatu Umar dai tace za ta dage a mulkin na ta wajen ganin an yi kokari a harkar noma da ilmi dsr.

Hindatu Umar ce mace ta farko da ta zama Shugaban Karamar Hukumar a Garin. A baya dai ana ta sukar ta da cewa ba ta dace da mulki ba. An dai nada wannan budurwa ne bayan wa’adin kwamitin rikon kwaryar da aka nada a baya ya kare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: