Amfanin bawon lemu

Amfanin bawon lemu

Bayan ka karanta wanna, bazaka kara zubar da bawon lemunka ba

Amfanin bawon lemu
Amfanin bawon lemu

Nan gaba idan ka sha lemu kuma kaje zubar da bawon, ka tuna amfanin abunda kake shirin zubarwa.

Bawon lemun da ake zubarwa suna da sinadari da amfanin da zai kawo wa jikinga ci gaba mai kyau.

Bayan amfanin sinadarin vitamin C da ake samu daga jikin lemu, bawon na da ikon gyara huhu yana kuma taimakawa gurin yaki da guba da zai iya kawo matsala ga huhu.

KU KARANTA KUMA: Abun farin ciki ya samu mai sana'ar sayar da madara

Lemu na dauke da sinadari masu gyara jiki sosai da kuma sa jiki aiki yanda ya dace. Bawon lemu na dauke da wani sinadari mai karfi da ake kira da Flavanones; suna kuma taimakawa gurin rage lalacewa ta hanyar hada abu da iskar da ake shaka.

Sinadarin vitamin C da lemu ke dauke da shi,yana taimakawa gurin gyara kalar jiki, yana kara wa fata haske da sheki.

Zaka iya busar da bawon lemu, ka hada da zuma da madarar youghort ka shafa a fuska, yana gyara fatar fuska sosai.

Ana kuma amfani dashi gurin kara hasken hakori, domin yana dauke da sinadarin dd-limonene, yana cire dattin hakori. Ya na kuma taimakawa gurin cire dattin sigari a hakori.

Suna kuma taimakawa gurin dauke wari, ta hanyar kona busashen bawon lemu, yana kuma ba da kamshi mai ni’ima da dadi.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng