Gwamna Jibrilla Bindow zai fasa kwai

Gwamna Jibrilla Bindow zai fasa kwai

- Gwamnan Jihar Adamawa Bindow Jibrilla zai tona asirin tsohon gwamnan jihar

- Gwamna Jibrilla yayi barazanar tona asirin badakalar Murtala H Nyako a lokacin da yake Gwamnan Jihar

- Gwamnan Jihar Jibrilla Bindow ya koka da mutanen Nyako da ke neman kawo masa cikas

Gwamna Jibrilla Bindow zai fasa kwai

 

 

 

 

 

 

Gwamnan Jihar Adamawa Jibrilla Bindow yace idan har aka matsa masa, to zai cirewa Tsohon Gwamnan Jihar Murtala Nyako zane a kasuwa. Gwamna Jibrilla yayi barazanar sa hannu a takardar da ke dauke da irin badakalar da Gwamna Nyako yayi lokacin yana mulkin Jihar. Gwamnan Jihar yayi wannnan bayani ne jiya kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rahoto.

KU KARANTA: PDP tace da Kotu ta tsige Gwamnan ta

Yayin da Gwamna Jibrilla na Adamawa yake tattaunawa da wasu magoya bayan sa, ya zargi magoya bayan Tsohon Gwamna Nyako da kokarin ganin bayan Gwamnatin sa. Gwamna Bindow Jibrilla ya bayyanawa cewa idan aka matsa fa, sai tona asirin tsohon Gwamnan Jihar-Mai gidan na su, Murtala Nyako. Nyako dai yayi Gwamna a Jihar ne kafin a tsige sa kafin wa’adin sa ya kare. Gwamna Jibrilla ya zargi Mutanen Nyako da kokarin kawo masa cikas a Gwamantin sa.

Gwamna Jibrilla yace yana da takardun da suke nuna irin barnar da aka tafka lokacin Gwamnatin Tsohon Gwamna Nyako. A cewar Gwamna Bindow Jibrilla, titin da ya gina a Garin Yola bai wuce Miliyan 600 ba, shi kuwa Nyako ya kashe fiye da Biliyan 2.6 wajen gina wani irin sa. Gwamnan Jihar Bindow Jibrilla, ya bayyana ire-iren wadannan badakala da aka samu a lokacin Gwamna Nyako.

Gwamna Jibrilla yace idan fa kura ta kai bango, to zai fasa kwai. An nada wani kwamiti karkashin wani Alkali Bobboi, wanda yayi bincike game da barnar da Gwamna Nyako ya tafka bayan an tsige sa. Gwamna Fintiri ne dai ya nada wannan kwamiti, takardar kuma tana nan yanzu haka, wanda Gwamna Jibrilla yace idan suka ce masa kule, zai ce cas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel