Fulani Makiyaya sun kai wata mumunan hari kauye
Wasu Fulani Makiyaya sun kashe kutane 3 ,sun jinkita 6 kuma sun banka ma kauye wuta a jihar Kaduna da kuma Fulanin makiyayan sun afka kauyen Godogodo.
Fulani makiyaya sun hallaka mutane 3 mazauna Dogon Daji da kuma Antang a godogodo ,karamar hukumar Jema’a a jihar Kaduna.
An kasance dai ana kai hari Godgodo ne tun watan yuli yayinda Fulani na ikirarin sun asalin mazauna wurin.
Wani mazauni kauyen yace: “ Da safen nan , wasu makiyaya suka kawo mana hari dogon daji. Sun kashe mutane 3 kuma sun kona wasu wurare sun raunata mutane.”
Amma,mukaddashin shugaban karamar hokum jama’a. Mista Humble Katuka, yace an kashe mutane 2 a Antang kuma an kona gida 1 Antang.
Yace: “Labarin da samu yanzu na cewa an kashe mutane 2 a Dogon daji kuma an kona gidaje 2 a Atang. Sun kawar da hankalin soji da yan sandan da ke godgodo ne kafin sukayi wannan aika-aikan.”
KU KARANTA: Wani dan bautan kasa ya mutu a Bayelsa
Amma jami’an tsaro sun gaggauto kuma zan je da kaina inga abinda ya faru.
Zaku tuna cewa an kai irin wannan hari a ranan asabar 2 ga watan satumba Godogodo inda aka kashe yan banga 4.
Jawabin da Kanal Sani Usman ya bada yace: “Rundunar division 1 a cikin wata harin da ta gudannar tare da yan sandan da yan banga a yau na wasu yan bindiga a Godogodo,a jihar Kaduna.
Jami’an tsaron sun kama wadannan mutanen : Lawal Gambo, Yau Sani, Bala Amodu, Ibrahim Maikaru, Abubakar Hassan da Bashiru Isa Ciroma. Amma , yan banga 4 sun rasa rayukansu kuma wasu 9 sun jinkata yayinda suke yunkurin kare harin da akayi domin asaran rayukan mutane da dukiyoyinsu.
Yanzu dai an kwantar da wutan kuma anan kokarin cimma wadanda suka arce a cikin yan barandan. Muna tabbatar wa jama’a cewa zamu kare rayuwarsu da dukiyoyinsu da kuma tabbatar da cewa an kama wadannan yan barandan.”
Asali: Legit.ng