Tanka ta fada kan karamar mota, mutum daya ya rasu
Wani mutum ya rasa ransa sakamakon hatsarin mota data rutsa da shi yayin da wata babbar motar tanka dauke da mai ta fada kan wata karamar mota.
Jaridar Daily Post ta ruwaito hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) tana cewa ta samu kiraye kiraye dangae da wata babbar mota data fadi daga wasu jama’a da safiyar ranar lahadi 25 ga watan satumba ta lambarta 767/112 dangane
Rahoton LASEMA ya bayyana cewa wata motar Tanka mai lamba AGL 664 XG, dauke da man fetur lita 33,000 dake gudun wuce sa’a mallakar kamfanin Forte Oil ta fada kan wata karamar mota kirar Hyundai yayin da take kokarin shan shataletale, sanadiyyar haka mutumin dake cikin karamar motar ya rasa ransa.
KU KARANTA:Amarya ta rasu da juna biyu wata daya dayin aure
Nan da nan jami’an tsaro mabanbanta kamar su rundunar tsaro ta farin kaya, LASTMA, LASEMA, FRSC da yansanda suka hallara inda hatsarin ya afku domin magance fetur din kamawa da wuta. Jami’an sun samu daman daga motar, inda aka ciro gawar mamacin, kuma aka garzaya da ita dakin ajiye gawa na asibitin Ikorodu. Daga bisani kuma aka dauke motocin daga kan hanya, inda aka mika su ga hukumar yansanda.
Sai dai shugaban hukumar LASEMA Adesina Tiamiyu yace za’a gudanag da cikakken bincike kan dalilin hatsarin, sa’annan ya baiwa direbobi shawarar dasu daina gudun wuce sa’a a kan tituna, tare da kula da dokokin tuki.
Asali: Legit.ng