Ma’aurata sun kirkiro Sabon salon sumbatar juna
Sabon salo, gemu a kafada inji Bahaushe, inda al’ummar nahiyar Afirka na daga cikin mutane masu matukar kaifin basira, musamman idan suka samu yanayi mai kyau.
A kwanan ne aka samu wasu ma’aurata da suka kirkiri wani sabon salon nuna ma juna soyayya a ranar aurensu.
Ma’auratan sun fito da wani sabon salon sumbatar junarsu ne, inda abokan angon suka daga ango sama, ita ma amaryar kawayenta suka daga ta daidai wajen ango, sa’annan suka sumbaci juna.
KU KARANTA: Hotunan ma’aurata na ban dariya
Wannan sabon salo dai yayi matukar baiwa yan kallo mamaki, ta yadda jama’a suka cika da sha’awar irin salon soyayyardake tsakanin angon da amaryarsa.
Sai dai har zuwa yanzu ba’a san hakikanin sunayen ma’auratan ba, amma tabbas hoton nasu ya kayatar da jama’a.
Asali: Legit.ng