Duk mai rai: Allah yayi wa wani matashin haziki dan baiwa, Lil Ameer rasuwa
Innalillahi wa inna ilaihirraji'un.Allah ya yi wa wani shahararren mawakin hip hop na Hausa mai suna Lil Ameer daga jihar Kano rasuwa a jiya Alhamis.
Mawakin dai kamar yadda muka samu daga majiyoyin mu da dama yaro ne mai hazaka da kuma tauraruwar sa ke cikin ganiyar haskawa a birnin na Kano dama wasu jihohin na Arewa kafin rasuwar tasa.
KU KARANTA: Kwamishinan yan sandan jihar Abia ya rasa mukamin sa
Legit.ng dai har yanzu ba ta samu ainihin takamaiman dalilin rasuwar ta sa ba amma dai ta lura cewa kafofin sadarwar zamani daga jiya zuwa yau sun cika da sakonnin ta'aziyya da jaje daga abokai da yan uwa da dama suna matukar nuna alhinin su da rashin da aka yi nashi.
Za'a yi jana'izar sa ya juma'a a kusa da masallacin dake unguwar Tarauni.
Allah ya jikan sa. Amin.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng