Hira da wani dan bautar Kasa 'NYSC' da yayi abin sha'awa

Hira da wani dan bautar Kasa 'NYSC' da yayi abin sha'awa

Hira da wani dan NYSC da ya kirkiro Manhajar kare hadari a Najeriya.

Hira da wani dan bautar Kasa 'NYSC' da yayi abin sha'awa

 

 

 

 

 

 

Wakilin Legit.ng Hausa mai suna Muhammad Malumfashi ya gana da Malam Musa Bello, wani matashi kuma mai hidimar Kasa (NYSC) a yanzu haka a Garin Minna, Jihar Niger. Musa Bello ya kera wata manhaja da za ta rage matsalar da ake samu idan an yi hadarin mota. Wannan manhaja ta waya na dauke da lambobin ‘yan kwana-kwana da za su ceci rai yayin da aka samu hadari ko a ina ne a Kasar nan.

Musa Bello mutumin Kaduna ne, ya rasa mahaifin sa tun yana karami. Musa yayi karatu ne Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, ya kuma kware sosai a harkar Ilmin Komfuta.

Wannan Manhajar tana dauke da lambobin Jami’an kwana-kwana da na tsaro, da dai sauran su, a duk inda mutum ya samu kan sa yana neman taimako, sai dai kawai ya dauka wayar sa, ya bude wannan manhaja yayi kira ko ya aika sakon gaggawa.

Musa Bello yayi hira da Muhammad Malumfashi na Legit.ng Hausa, ga dai yadda muka yi da shi.

KU KARANTA: Ko mulkin Najeriya gadon gidan Arewa ne?

Legit.ng: Barka dai.

Musa Bello: Barka da.

Legit.ng: Ko za ka iya bamu takaitaccen tarihin rayuwar ka?

Musa Bello: To.

Musa Bello: Da farko sunana Musa Bello, an haife ni a Ranar 19 ga watan Nuwamba a shekarar 1992. Asali na mutumin Garin Zaria ne a Jihar Kaduna. Gidan mu, mu 6 ne, ni ne kuma na biyun karshe. Nayi digiri a Jam’ar Ahmadu Bello ta Zaria. Nayi karatun Firamare na a Makarantar ‘Mameena Memorial’, na kuma yi Sakandare a Makarantar ‘Kaduna Polytechnic Demonstration Secondary’ da ke Kaduna.

Legit.ng: Watau a Jihar Kaduna dai kayi duk karatun ka, ba ka taba fita waje ba?

Musa Bello: Abin ai sa rai ne, ban taba fita wata Kasa ba.

Legit.ng: Ya Garin Kaduna yake ne?

Musa Bello: A Jihar Kaduna akwai dama da da yawa, ya rage mutum….

Legit.ng: Dama an ce Kaduna gidan ilmi!

Musa Bello: Kwarai! Haka abin yake.

Legit.ng: Ya, ko za ka iya tuna yarintar ka?

Musa Bello: Toh…yarinta akwai dadi sosai. A lokacin nan ni da wasu abokai na; Fahad Bello Turkur, da Umar Isa Suleiman mu kan hada motocin katako, da injin keke. Mahaifina kuma ya rasu ina yaro, shekarar 2006. Na kuma je makarantar Islamiyya mai suna Madrasatul Rafa'ud Dinul Islam (Dan Hausa).

Legit.ng: Allah ya jikan sa. Mahaifiyar ka ce tayi dawainiyar ka kenan?

Musa Bello: Tun bayan rasuwar sa, Uwar mu ta ke kula da mu. Ta sha wahala da mu sosai. Sunan ta kuwa Hajiya Maryam Bello.

Legit.ng: Kace ba Komfuta kadai ba, ka ma san karatun Muhamadiyya, naga kayi Islamiyya…

Legit.ng: Ko yaushe ka fara amfani da Komfuta?

Musa Bello: Tun ina Firamare na fara amfani da na’urar Komfuta.

Legit.ng: Kace abin ba yau aka fara ba?

Musa Bello: Na dade ina so in zama mai kirkirar Manhajar Komfuta ai.

Legit.ng: Madalla!

Musa Bello: Ina da burin haka, na kuma dai hada da addu’a.

Legit.ng: Ya ka tsinci kan ka a Jami’ar A.B.U?

Musa Bello: Na dan sha wahala a ABU Zaria gaskiya, karantar ilmin Komfuta akwai dan wahala. Sun yi kokari wajen koya mana yadda ake amfani da ita.

Legit.ng: Da kyau!

Legit.ng: Ko kana da niyyar zuwa karo karatu, watau Digiri na biyu?

Musa Bello: Eh, gaskiya ina da niyya. Sai dai har yanzu ban gama yanke shawarar inda zan je ba. Abin da nake so, in je inda zan koyi aiki sosai, in kware a wajen wasa da Komfutar.

Musa Bello: Ni fa abin da nake so, ba sai wai Gwamnati ta bani aiki ba, ni da kai na, in rika neman kudi na. Wasu ma kuma su ci abinci a kasa na.

Legit.ng: Ko a ABU kadai kayi karatun Komfuta ne?

Musa Bello: A’a ba nan kadai ba, a nan dai na fara, amma na karanta wasu kwas dabam a wasu wuraren.

Legit.ng: Irin su wane kwas-kwasai kayi?

Musa Bello: Suna da yawa kam. Akwai: Information Security (Ethical Hacking), Mobile Apps Development using C#, Diploma in computer maintenance, Diploma in computer networking, Certificate in Web Development using Drupal, Certificate in Database Management System using MySQL, Diploma in computer operations, Certificate in Computer maintenance da dai sauran su.

Legit.ng: Lallai ka san Komfuta!

Musa Bello: Ina da sha’awar abin kam.

Legit.ng: To ya kuma harkar hidimar Kasa ‘NYSC’?

Musa Bello: NYSC akwai dadi, kullum kana kara koyan wani abu nea rayuwa. Yanzu haka ina koyan wasu ilmin na dabam da suka shafi harkar bidiyo.

Legit.ng: Watau ba dai ka zama haka nan, sai an dan taba abin?

Musa Bello: To ya za ayi!

Legit.ng: Ina kake aikin ne?

Musa Bello: Tashar Talabiji na NTA Minna.

Legit.ng: Kana harkar aikin bidiyon kenan.

Musa Bello: A’a, haka dai suka so, amma wani aikin dabam na ke yi.

Legit.ng: Ya ka samu Garin Minna?

Musa Bello: Garin Minna sai hamdala, babu rikci, sai dai fa matsalar su daya, rashin wuta. Amma ina jin dadin Garin kwarai da gaske.

Legit.ng: Gaskiya ana kuka da rashin wutar, duk da cewa suna da ruwa da suke jawo wutar lantarki…Ai kamata yayi ka kirkiro masu wata na’ura da za ta magance wannan!

Legit.ng: ? *Dariya*

Musa Bello: HAHAHA!!!

Legit.ng: To ina maganar Manhajar ka? Wai meyasa ka kirkire ta ne?

Musa Bello: Ka san so da yawa sai kaga an yi hadari bisa titi amma ba a san yadda za ayi ba. Wani lokaci hakan ya taba faruwa da ni, wani ya samu hadari, sai na nemi lambar ‘yan kwana-kwana, kafin kace mene, sai aka zo aka cece sa. Mutane kuwa da dama ba su san wannan ba, suka yi ta mamaki, tun daga wannan lokaci na sha alwashin kirkirar wannan abu.

Legit.ng: Ka ga wannan zai ceci rayuwa da dama.

Musa Bello: …Kwarai da gaske, dubi wurin hadarin titi ko gobarar wuta, ko inda ake neman Jami’an tsaro. Nan take mutum zai tuntube su daga wayar sa.

Legit.ng: Jihohi irin su Legas kam suna da kokarin wannan, Ko Jihar Neja ma suna…?

Musa Bello: Eh na san Legas sun yi nisa, amma dai Neja da saura tukun.

Legit.ng: Muna fata su bi sahu..

Legit.ng: Kyauta ake sauke manhajar?

Musa Bello: Ko sisi kuwa, kyauta ta ke.

Legit.ng: A ina zan same ta?

Musa Bello: Ai da kaje Google Play tana nan, sai dai kawai ka nemi ‘Distress call app’ ka sauke.

Legit.ng: Ganin cigaba ya samu, wani taimako kake tunanin Gwamnati ya kamata tayi maka game da wannan fasaha?

Musa Bello: Ta goyi bayan wannan abu, ta karfafa mani. Kaga idan za a rika talla a kafafe ana nuna amfanin sa, da an kyauta. Kuma zan so a bani lambobin sauran masu bada agajin kar-ta-kwana. Yanzu haka ina neman lambobin Hukumar KASTELEA ta Kaduna.

Legit.ng: Ga shi yanzu ka shiga duniya...

Musa Bello: Eh Gaskiya. Burina ace, duk inda mutum ya je, idan yana bukatar neman wani taimako; idan yayi hadari, ko motar sa ta tsaya, ko yana neman Jami’an tsaro, ko a ina a Najeriya, yayi amfani da wannan manhaja.

Legit.ng: Da kyau kuwa.

Legit.ng: Me za kace ga masu tasowa irin ka? Don aikin ka ya ba su sha’awa.

Musa Bello: Su dage da bincike sosai domin su taimaki al’umma, su kuma rike addu’a, itace kan gaba!

Legit.ng: A karshe, mai kake nema Gwamnati tayi maka?

Musa Bello: Su taimake mu wajen kara sanin aiki, don mu ma mu taimaki wasu, mu koya masu. Ba na bukatar wani aiki daga Gwamnati, sai wannan. A haka, ka ga za a rage yawan matsalar aikin yi.

Legit.ng: Muna fata, Gwamnati ta duba wannan lamari.

Musa Bello: Muma fatan namu kenan.

Legit.ng: Mun gode da ka yi wannan hira da mu, Legit.ng.

Musa Bello: Babu damuwa, nima na gode.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel