Motar haya ta fada cikin rafin Rijana a hanyar Kaduna

Motar haya ta fada cikin rafin Rijana a hanyar Kaduna

– Wata babban motan haya ta fada rafin Rijana a hanyar Kaduna-Abuja

– Mutane 3 ne suka rasa rayukan su a hadarin

– Mutane 14 ne suka bace, duka da dai ana neman su

Motar haya ta fada cikin rafin Rijana a hanyar Kaduna

Mota mai kujeru 18 ce ta fada rijiya a hanyar Kaduna-Abuja, kuma mutanen 3 ne suka rasa rayukansu.

Shiyar hukumar kula da tsaron hanyoyi ta Kaduna FRSC ta tabbatar da mutuwan mutane 3 kuma an alanta bacewan mutane 14.

Game da cewar shugaban aiki,Mr Salisu Galadanci, yace haarin ya faru misalign krfe 11 na daren ranan talata. Galadanci ya fada ma manema labarai a ranan laraba cewa mutane 18 yan gida daya ne masu dawowa Lokoja daga Kano ne sukayi hadarin.

Game da cewar sa,mutum daya ne kawai ya sham an gano gawawwaki 3. Wata mota mai kujeru 18 mai tafiya daga Kano zuwa Lokoja ta fada rafin Rijana.

KU KARANTA: Hira da wani dan bautar Kasa ‘NYSC’ da yayi abin a zo-a gani

“Mutum daya data tsallake rijiya da baya ne ta sanar da Hukumar FRSC da ke doka Unit,a hanyar Kaduna – Abuja misalin karfe 7 na safe aranan Laraba.

“Masu ceto mutane dake Doka, Katari, Kakau ne aka tura da kuma taimakon direbobi domin nemo su. Amma gawawwaki 3 kawai aka gani, ba’a ga sauran ba, har da ‘yar wacce ta tsira.

Ya kara da cewa wanda ya tsiran tace hadarin ya faru ne lokaci daya, kuma sanadiyar gajiya ne da gudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng