Ko shin mulkin Kasar nan gadon Hausa-Fulani ko Arewa ne?
Mulkin Kasa: Yaushe ya zama gadon ‘yan Arewa?
An hade Kasar Najeriya ne fiye da shekaru dari da suka wuce, wannan hadin da Turawa dai suka yi bai wuce a takarda ba, Inji wani Tsohon Shugaba a Kasar, shi kuwa Sardauna kiran wannan hadin gambizar ma yayi da ma kuskure. Don kuwa tun a wancan lokaci Najeriya na da miliyoyin mutane dabam-dabam, akwai kabilu fiye da 200. Sai dai Turawa ba su damu ba, idan har bukatar su, za ta biya. Daga samun ‘yancin kai a shekarar 1960 zuwa yau (Kusan shekara 56), Arewacin Kasar kadai ta mulki Najeriya na kusan shekaru 40! Wanda wasu na ganin abin ya zama tamkar dai gadon gidan su!
Mutanen Arewa na Hausa-Fulani sun dade suna mulkar Kasar.
Hausa-Fulani a Arewacin Najeriya
Duk da cewa akwai kyakkyawar alaka tsakanin Hausa da Fulani a Kasar nan, sai dai wannan Kalmar ta ‘Hausa-Fulani’, ‘Yan Jaridun Kudancin Kasar nan ne suka fara kirkiro ta, don wani burina siyasa. A wajen su duk wanda bai tsallaka gadar Jebba ba, ya zama Hausa-Fulani; da Banufe, da Babarbare, da Bagwari, da Babushe, da Bakatafe, da Babole, da Ba’ame da Bagizime duk Hausa-Fulani ne kawai! Hakan zai sa ka fahimci dalilin da ake kallon Abubakar Tafawa-Balewa, Yakubu Gowon, Ibrahim Babangida, Sani Abacha, Abdussalami duk a matsayin Hausa ko Fulani (Ko duka, kamar yadda suka hada)
Hausa-Fulani suna sallar Jumu’a a garin Sokoto a wajen shekarar 1956
Mulkin Mallaka
Lokacin da Turawan Kasar Ingila na mulkin mallaka suka raba Kasar, sai ya zama Arewa ta fi ko ina girma. Bari ma, ta fi dukkanin bangaren kudancin Kasar, wasu suna ganin da gan-gan aka yi hakan. Ko da ma can Turawa ay a mulki Malam Bahaushe kai tsaye ba, sai dai suka yi amfani da Sarakunan su. Mafi yawancin mutanen Arewa musulmai ne, kuma Hausawa (kusan sama da kashi 70 bisa 100), domin addinin musulunci ya shigo Kasar tun kusan shekaru 500 baya. Yayin da su kuma ‘Yan kudancin Kasar sai suka rungumi Turawan hannu biyu, da dama suka bar addinin ay a gargajiya suka bi addinin Kiristanci, da ma duk abin da aka yi masu talla.
An yi fafutukar neman ‘Yancin Kasar nan, wanda ya kai aka samu a Ranar 1 ga watan Oktoban 1960 (Abin da ya sa aka kawo ay aba, domin ‘Yan Arewa ay a shiryawa mulki a ay aba). Wani bincike ya nuna cewa bai wuce kashi 2% na ‘Yan Arewa suka san Boko ba (Duk da cewa sun yi karatun Ajami). Da aka shirya siyasa kuwa, sai Mutanen Arewa suka kafa Jam’iyyar NPC, A kudu-ta-yamma kuwa a ka shiga AG, ta su Awolowo, yayin da mutanen su Zik watau Inyamurai suka bi bayan NCNC. Da aka tambayi Ahmadu Bello game da halin siyasar, sai yace ai tuni zai murkushe su Awolowo, hakan kuwa aka yi! Duk da cewa ana ganin su koma-baya, amma da yake abin yawa ake bi, Arewa ta mamaye siyasar Kasar. Ko da yake Jam’iyyar NPC ta su Sardauna ba ta samu rinjayen da ake bukata ba (amma ta fi kowace Jam’iyya rinjaye a Majalisa) sai aka shiga hadin-kai da Jam’iyyar NCNC ta su Arzikwe, aka kafa Gwamnatin hadaka. Arewacin Kasar na mulki, Yarbawa; su Awolowo suna adawa.
KU KARANTA: Siyasa da tattalin Arzikin Arewacin Najeriya bayan 'Yancin Kai
Marigayi Sardaunan Sokoto, Sir Ahmadu Bello Kenan
Jamhuriya ta daya
Abubakar Tafawa-Balewa ya zama Firayim-Minista, shi kuma Nnamdi Arzikwe ya zama Shugaban Kasa (duk da cewa a suna ne kurum). An ta samun korafai na cin hanci da rashawa daga wajen ‘Yan Siyasar Kasar. An kai ma Balewa kukan satar da wasu Ministoci suke tafkawa, sai dai abin ya fi karfin sa, domin kuwa idan yayi wani yunkuri, Gwamnati za ta watse (tun da hadaka aka yi). Bayan an kara gudanar da zabe Jam’iyyar NPC ta Mutanen Arewa ta kara lashe zaben. Kafin nan an samu rikicin siyasa ya barke a Bangaren Yarbawa, har ta kai an kafa dokar ta baci, a wannan yanayi an samu juyin hali. Daga nan wasu suka fara kokarin ganin bayan wannan Gwamnati.
Firayim Minista Balewa tare da Shugaban Kasar Amurka John Fitzergald Kennedy
Juyin Mulkin farko da na biyu
A watan Junairun shekarar 1966 aka yi juyin mulkin farko a Kasar, wasu (mafi yawancin su) ‘Yan kabilar Ibo suka hambarar da Gwamnatin Balewa, suka kuma kashe su Sardauna da manyan Sojojin Arewa. Haka kuma, an kashe wasu kadan daga cikin ‘Yan siyasar kudun (Irin su Ministan Kudi Festus Okotie-Eboh), amma kusan duk wani Inyamuri da ke mulki ko gidan Soji ya sha! Masu juyin-mulkin sun yi kokarin kawo sauyi a Kasar, a cewar su, game da yadda ‘yan siyasa suka shiga facali da dukiyar Kasa tsakanin su. Sai dai an samu taka masu birki. Wani kuma Inyamurin ne dai ya dare mulkin Kasar, Shugaban Hafsun Sojin Kasar, Janar Aguyi-Ironsi.
Bayan kisar su Firamiya na Arewa, Sardauna, kuma Aguiyi-Ironsi ya hau mulki, Hausawa sun ga wulakanci da muzanci a Kasar. Shugaban Kasan bai kuma dauki wani mataki ga wadanda suka kashe manyan Arewan ba (Irin su Major Nzegwu, wanda ya zauna gidan Firimiya kuma shi ya kashe Sardunan). ‘Yan Arewa ba su gama hucewa ba, suka kama Ironsi suka kashe, sun hambarar da Gwamnatin sa cikin wata shida. Bayan wannan juyin-mulki na gayya, wani Sojan Arewar ya samu darewa mulkin Kasar.
Major Nzeogwu ‘Kaduna’ wanda ya tashi gidan Sardauna, daga karshe kuma shi ya kashe Sardaunan
Mulkin Gowon da rikicin Biafra
Yakubu Gowon, babban Sojan Arewa a wancan lokaci, wanda kuma ya taka rawar gani wajen hana juyin mulkin farko, ya zama Shugaban Kasar, duk da cewa yaro ne shakaf! Sai dai fa hakan bai yi wa Kanar Ojukwu dadi ba, yana ganin shi ya fi dacewa, Ojukwu mutumin Kasar Ibo ne.
Gowon da Ojukwu a Aburi (kasar Ghana) wata guda kafin a barke da yakin Biafra
Bayan Juyin mulkin gayyar da Hausawa suka yi, Inyamurai sun fara gamuwa da barazana game da rayuwar su a Arewacin Kasar, kai har ta kai, suka fara tserewa suna barin kayan su. Ganin hakan ne Ojukwu yaga cewa Shugaba Gowon (wanda haifaffen Kiristan Zariya ne) ba zai iya kare ran mutanen Ibo ba, don haka ya nemi ballewa daga Kasar Najeriya. Bayan an-kai-an-komo, aka shiga gwabza yaki na basasa tsakanin Sojojin Ojuwkwu na Biafra da kuma Sojojin Najeriya. Bayan kusan shekaru biyu da rabi ana fafatawa, yunwa ta tagayyara ‘ya ‘yan Biafra, Ojukwu ya sulale, aka tsaida wutar yaki, aka sasanta. Aka dawo kamar dai ba ayi ba!
Wasu Inyamuran dai suna ganin Sojojin Najeriyar irin su Murtala Muhammad, M. Shuwa, Shehu ‘Yaradua, Obasanjo, Muhammadu Buhari, Babangida, Sani Abacha sun yi masu kisan gilla ne kawai don sun nemi su fice su bar Kasar Najeriya.
Tutar kasar Biafra da kuma takardar kudin su a wancan yunkuri, sun shiryawa ballewa daga Kasar
Abin da ya biyo bayan yaki
Kasar Biafra ta dawo Najeriya, ba nan kadai ba, sai da Inyamuri ya zama na biyu a duk Najeriya bayan wani dan lokaci. Shugaba Gowon yayi kokari wajen gyara barnar da aka yi wa Kasar. Bayan nan kuma ya kasa cika alkawarin sa na sauka daga mulki. Daga nan ne wasu Sojojin Arewacin Kasar suka hada kai suka hambarar da Gwamnatin sa yayin da ya bar Kasar. Murtala ya karbi mulkin Kasar, ya kuma kawo shirin gyara gadan-gadan, sai kai kafin yayi nisa aka ga bayan sa. Bayan an kashe Murtala bayan watanni shida da karbar mulki, sai mataimakin sa ya karba, Janar Obasanjo. Obasanjo yayi kokarin karasa ayyukan Murtala, duk da kuwa cewa bayarabe ne, wasu na ganin ai ‘Yan Arewa, mataimakan sa, TY Danjuma da Shehu Yar’adua ne kawai suka yi mulkin. Bayan an yi zabe, Janar Obasanjo ya dauki mulki da hannun sa, ya mika ga masu farar hula, abin da ba a taba yi ba a Najeriya, kai! Yammacin Afrika!
Janar Murtala; Kwanaki 200 rak yayi a kan Mulki, ya kara wasu Jihohi kuma ya kirkiro Kananan Hukumomi
An dawo Mulkin farar hula
Uku daga cikin manyan ‘yan takarar zaben Shugaban Kasan na 1978, za a iya kiran su Hausa-Fulani (duk da dai ba haka ainihin abin yake ba). Sauran ‘Yan takarar kuma sune; Zik dai wanda ya fito karkashin NPP (wanda Jam’iyyar NCNC ce ta rikida) da kuma Awolowa shi kuma karkashin UNPP (wanda a zahiri, tsohuwar Jam’iyyar AG ce) sai Shehu Shagari wanda ya lashe zaben a karkashin Jam’iyyar NPN (kusan ace dai tsohuwar NPC ta su Sardauna ta hada kai da wasu). Wannan karo ma dai su Awo da Zik ba su samu nasara ba kan Hausawa.
Yarbawa dai musamman, ba su ji dadin faduwa zaben ba. Sun zargi Janar Obasanjo da Hukumar zabe ta Kasa da wata manufa, abin har ya kai ga Kotun Koli. Su kuwa Inyamurai sun samu Mataimakin Shugaban Kasa, Alex Ekwume. Shugaba Shagari yayi kokari wajen samun daidaito wajen raba dama da duk mukaman Kasa, ya zama ba a cuci dan Arewa ba nan gaba. Sai dai abubuwa fa sun tabarbare ainun lokacin Shagari, cin hancin da aka yi da, ya zama wasan yaro. Da aka gudanar da zabe a shekarar 1983, Jam’iyyar su Shagari ta kara lashewa, sai dai wannan karo, an zuba magudin tsiya!
Shugaban Kasa Shehu Shagari tare da Sarauniyar Ingila a wajen 1983
Soji Sun dawo!
‘Yan Arewa ne dai suka kara karbe abin daga hannun ‘dan Arewa; ja ya fado, ja ya dauka! Sojoji ba su yi nisa can ba a Bariki, bayan da abin yayi kamari sai suka kutso kai! Janar Buhari ya zama Shugaban Kasa bayan Juyin mulkin Soji. Janar Tunde Idiaghbon ya zama mataimakin Shugaban Kasar na Soja (Shi ma kuma Musulmi, wasu ma na masa kallon Bafullatanin Ilorin ba Bayarabe ba). Suka shiga gyaran Kasar musamman game da harkar cin hanci dsr, tun can an san Buhari da gaskiya da rikon amana. Gwamnatin Buhari ta shiga kame manyan ‘Yan siyasar Kasar har sai sun kwaci kan su (musamman na Jam’iyyar UPN da NPN); daga kaji wanda za a daure shekara 150 sai mai 200 a gidan yari. Janar Buhari dai Najeriyar ya sa a gaba; Buhari ya bindige ‘yan fashi da makami da masu cinikin kwayoyi, ‘Yan Jaridu ma sun ga ta kan su a wannan mulki!
Janar Muhammadu Buhari da Janar Tunde Idiagbon sun karbe mulki
Zamanin Babbangida
Ba a cika watanni ashirin ba, wasu daga cikin na kusa da Janar Buhari suka hambarar da shi, su ka kuma garkame shi. Har wa yau kaji, wani dan Arewar ne dai ya kara karbe mulkin Kasar, Janar Ibrahim Babangida. IBB ya dade yana mulki, ya kawo cigaba musamman na tituna da sauran gine-gine a zamanin sa a Kasa baki daya, ya kuma karbo bashi daga Yamma (abin da Buhari ya ce a’a). IBB mutumin Jihar Neja, ya kirkiro sabbabon Jihohi a Kasar.
A shekarar 1990 aka ga dai cewa IBB ba sa da ranar sauka daga mulki, wani daga cikin Sojojin Kasar ya shirya kifar da Gwamnatin! Manjo Okar (wanda Mutumin Kudancin Kasar ne) yace yaga alama cewa ‘Yan Arewa sun dauki mulkin Kasar gado, abin da suke so, su yi ta mulkar sauran (Kudanci da Tsakiya) ‘Yan Kasar… Manjo Gideon Okar ya shirya hambarar da Gwamnatin IBB ya kuma hana ‘Yan Arewa Shugabancin, sai dai an ga bayan sa, hakan dai ya faru da wani babban Soja kuma aminin Shugaba IBB watau Mamman Vatsa.
A zamanin IBB Najeriya ta shiga cikin tawagar Kasashen musulunci watau IOC a boye. A lokacin ne kuma aka soke zaben Abiola, bayan alamu sun nuna cewa ya buge Bashir Tofa (Mutumin Kano, Hausa-Fulani) war-was! Hakan dai ta sa ba girma, ba arziki, IBB ya bar mulkin.
Janar Ibrahim Badamasi Babangida cikin kayan gida. Ya dade a kan mulki, daga shekarar 1985 har zuwa 1993
Daga Shonekan zuwa Abacha
IBB ya mika mulkin Kasar ga Gwamnatin rikon kwarya ta Cif Shonekan, shi Ernest Shonekan dan kasuwa ne a Legas. Kafin a fahimci alkiblar Kasar, tuni Janar Sani Abacha ya kara juya mulkin. Wasu dai dama sun ce da gan-gan Janar IBB ya bar Janar Sani Abacha a Gwamnati, shi kuwa dai yace sam ba haka abin yake ba.
Janar Abacha ya rusa Majalisu da duk wani tsarin Damokaradiyya na Kasar, yayi kokarin hada taron ganin inda Kasar ta dosa. Daga nan kuwa dai ya shiga kama wasu tsofaffin Sojojin Kasar (Har da irin su Janar Obasanjo da Yaradua, wanda sun rike mulkin Kasar). Janar Abacha kuma ya kama Abiola bayan ya bayyana kan sa a matsayin Shugaban Kasa. Zamanin Abacha ya murksuhe mutanen yankin Ogoni. Janar din ya hada kai da Shugaba Gaddafi na Kasar Libiya har Najeriya ta shiga sahun wasu Kasashe 8 masu tasowa. Abacha ya zama gagarabadau, sai da ya kai dai Turai tayi baran-baran da Abacha. Kwatsam! Sai ya mutu! Wasu dai na ganin ya gyara tattalin arzikin Kasar a lokacin sa, ana dai zargin kuma cewa ya saci kudi na hauka a Gwamnati!
Sojan yaki: Janar Sani Abacha ya kifar da Gwamnatin rikon kwarya
KU KARANTA: Manyan Yan Arewa da ba za a manta da su ba a Tarihi (Hotuna)
Abdussalami ya dawo da farar hula
Bayan mutuwar Abacha, Shugaban Hafsun Soji na Najeriya, Janar Abdussalami Abubakar yayi maza ya haye mulkin. Sai dai yayi alkawarin dawo da siyasar damukaradiyya Kasar, hakan kuma yayi, bayan shekaru ashirin ana fama da masu khaki. Sai dai mutane da dama har da irin su Babban Lauyan nan, Gani Fawahemi ya kai karar Shugaban Kasar, saboda yadda aka rika gudanar da mulkin Kasar na dan wannan lokaci, an maida Inyamurai saniyar ware. Manyan Hukumomi da ma’aikatun Kasar irin su; NPA, NNPC, NEPA, FSC, NIS, NPS, NITEL, dsr duk suna hannun Hausa-Fulani.
Tsohon shugaban kasa da mataimakin sa kenan; Obasanjo da Atiku Abubakar
Obasanjo zuwa Yar'Adua da Jonathan
A 1999 aka gudanar da zabe Obasanjo, bayan ya fito daga gidan yari ya lashe zabe, ya buge wani bayaraben watau Cif Olu Falae. Wasu na tananin cewa yarjejeniya ce aka yi na zai mika mulki ga Hausa-Fulani idan ya kamala wa’adin sa (ko dama dai IBB zai so ya fanshe kan sa daga maganar soke zaben Abiola wajen yarbawa). Ko da Obasanjo yaji dadin mulki, sai yayi mursisi, har ya nemi tazarce na uku. Da wannan yunkuri bai yiwu ba, sai ya kakaba Ummaru ‘Yaradua da mataimakin sa Goodluck Jonathan.
Umaru ‘Yaradua Hausa-Fulani ne (Danuwan Aminin Obasanjo, Shehu ‘Yaradua) shi kuwa bai taba sa ran mulkin Kasar ba, ya zama shugaban Kasa a 2007, bayan ya buge wasu manyan ‘Yan takarar duk ‘Yan Arewa; Atiku Abubakar na AC da Muhammadu Buhari na ANPP a Jam’iyyar su ta PDP. An dai tafka magudin da ba a taba irin sa ba a wannan zabe, da bakin sa, sai da ya fadi kusan hakan.
Yar’adua yayi kokarin kawo sauyi a Arewa da ma Najeriya sai dai ya samu matsalar tattalin arziki na duniya da rashin lafiyar da ta ci karfin sa. A lokacin nan mataimakin na sa Goodluck Jonathan, bai san abin da yake faruwa ba, asali ma ‘Yaradua ya wuce asibiti ba tare da ya bar mukaddashi ba. Wasu masu kishin Kasar (har da ‘Yan Arewa) su ka matsa, har sai da aka nada Jonathan rikon kwarya. Bayan ‘Yaradua ya rasu a watan Mayun 2010, aka tabbatar da Jonathan Goodluck Shugaban Kasan Najeriya.
Allah Sarki: Marigayi Shugaban Kasa, Ummaru Musa Yar’adua
Jonathan na hawa, ya kafa Gwamnati, ya kuma tsaida wasu ayyukan da Marigayi ‘Yaradua ya fara a Arewan da fadin Kasar. Bayan ak are wa’adin ‘Yaradua, ya nemi tsayawa takarar kan sa, wanda ya saba yarjejeniyar jam’iyyar PDP ta kama-kama. Haka kuwa yaci zaben, ya buge wasu ‘Yan Arewa, irin su Muhammadu Buhari dai na CPC, Nuhu Ribadu da Ibrahim Shekarau. Sai dai a lokacin sa rikicin Boko Haram yayi kamari kwarai, mutane dubannai suka rasu, wasu kuma da dama suka gudu ko aka sace su. Cin hanci da a Kasar ya zama abin ba a Magana kawai! Hakan dai ta sa aka zabi Muhammadu Buhari.
Muhammadu Buhari
Wanda ake yi wa lakabi da na talawa, Buhari yayi mulki a baya, ya kuma nemi ya dawo har karo uku. Ya samu nasarar buge Shugaban Kasan da ke ci bayan sun kafa Jam’iyyar hadaka (tsakanin ‘yan adawa). Buhari dai ya tsaida rikicin Boko Haram da ke kashe mutane da sunan addini da hawan sa. Sai dai yanzu Kasar, musamman Arewa ana fama da matsalar yunwa da rashin kudi a kasa. Shugaba Buhari dai yace dole a koma noma a Kasar domin samun abinci. Tuni kuma Shugaba Buhari ya bada umarnin a fara nemo mai a Yankin Arewan.
Wasu kuwa suna ganin Shugaba Buhari wanda Hausa-Fulani ne na neman ganin bayan su; ko ta hanyar Makiyaya ko ta wata hanyar dabam. Su kuwa ‘Yan yankin Neja-Delta masu arzikin mai, tuni suka shiga barna, suna fasa butatan Kasar. Shugaban dai yace ko su ji su daina, ko jikin su ya fada masu. A mulkin sa an rufe irin su Sambo Dasuki (Su Dasuki ne suka kifar da Gwamnatin Buhari a 1985) da zargin satar kudin makaman Kasar, haka kuma ana daure da Shugaban Shi’a, Ibrahim Zakzaky da kuma Shugaban Kungiyar IPOB ta Biafra Nnamdi Kanu, wata da watanni.
Tsohon Shugaban Kasa Jonathan tare da Shugaba-na-yanzu, Muhammadu Buhari
Kammalawa
Wasu dai suna da ra’ayin cewa ‘Yan Arewa ko dai Hausa-Fulani sun dauki mulkin Kasar kamar gado, su kadai suka iya! Duk da wasu na ganin ‘yan Arewa a matsayin koma-baya ko kuma ci-ma-gari-banza; sai dai a hako mai a Kudancin Kasar, a ba su, a bulus. Mafi yawancin wadanda suka mallaki rijiyoyin mai a Kudancin Kasar, ‘Yan Arewan ne. A baya, an koka da yadda Hausa-Fulani su ka mamaye gidan Sojin Kasar da ma Hukumar ‘Yan Sanda. Har yanzu dai wasu na kukan cewa Hausa-Fulani suna murkushe su. Sai dai kusan gaskiyar maganar ita ce, masu mulki duk suna murkushe mu gaba daya a sama. Idan aka duba wani lokaci za ka ga ba abin da Shugaba yayi wa yankin sa, watakila dai mutanen sa, za su samu kudi!
Asali: Legit.ng